✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa direbobin J5 zanga-zanga a Binuwai

Deribobin sun bukaci gwamnatin jihar Benuwai ta shiga lamarin.

Direbobin motocin J5 da ke daukar kayan gwari daga garin Gboko na Jihar Binuwai zuwa sassa daban-daban na kasar nan sun yi zanga-zanga tare da tare babbar hanyar shiga garin.

Direbobin sun ce sun yi zanga-zangar ne sakamakon tursasawar da matasan yankin ke yi musu suna karbar kudi a hannunsu.

Da yake zantawa da Aminiya kan lamarin, Shugaban Kungiyar Direbobin Motocin J5 na garin Gboko, Malam Muhammed Mahe Alhassan Kwaftara, ya yi karin haske a kan dalilin zanga-zangar.

  1. Matsalar Tsaro: An bukaci Fulani makiyaya su yi wa dabbobinsu lamba
  2. An kama ‘barawo’ yana bikin zagayowar ranar haihuwarsa

“Akwai wata kasuwa a hanyar Ribas zuwa Binuwai; idan direba ya dauko kaya sai ya hadu da shingayen wadannan matasa ‘yan iska sama da 20 kuma duk shinge sai ya biya kudi N5,000 kafin ya wuce ko kuma a yi masa duka.

“Mun kai kokenmu ga jami’an tsaro da sarakunan wannan yanki don a dauki mataki kan wannan al’amari amma ba a iya yin komai ba.

“Don haka muka fito wannan zanga-zanga har sai Gwamna ya zo ya ga abin da yake faruwa, don ya dauki mataki.

“Don mu ma ‘yan Najeriya ne, muna da hakki a kansa na ya kare mu,” a cewar Mahe.

‘Sai Gwamna ya zo’

Ya ce sun shiga zanga-zangar ne saboda kayar da motarsu da matasa masu saka shinge suka yi a kan hanyar Ribas zuwa garin na Gboko.

Motar J5 da matasa masu sanya shingaye suka kayar a hanyar zuwa Gboko

Ya kuma ce faduwar motar ta haddasa wa mutanen da ke ciki munanan raunuka lokacin da lamarin ya faru.

Wani daga cikin mutanen da suke cikin motar da aka kayar
Wani daga cikin mutanen da suke cikin motar da aka kayar
Wani daga cikin mutanen da suke cikin motar da aka kayar

Mahe ya bayyana cewa a kullum sukan yi safarar kayan gwari mota 150 zuwa 200, zuwa garuruwan Kano, Maiduguri, Katsina, Sakkwato, Fatakwal, Kalaba da sauran sassa na Najeriya.

Ya ce amma babbar damuwarsu a garin ita ce matasa na cin zarafin direbobinsu, ta hanyar sanya masu shingaye a kowanne kauye inda suke karbar kudade daga wajensu.

Direbobin motocin na J5 sun fito da motocinsu ne suka rufe babbar hanyar shiga garin, da misalin karfe 6 na safiyar ranar Laraba har zuwa wayewar ranar Alhamis.

Wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai, Sewuese Kate Anene, ta waya don jin ta-bakinta kan al’amarin.

Amma ta aiko da rubutaccen sako ta waya cewa zuwa wannan lokaci ba ta samu labarin faruwar lamarin ba.