✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direbobin tanka sun toshe hanyar Kano-Zariya

Kwana guda bayan zargin soja da harbe wani direban tanka a hanyar Zariya zuwa Kano, direbobin tanka sun rufe hanyar don gudanar da zanga-zanga. Da…

Kwana guda bayan zargin soja da harbe wani direban tanka a hanyar Zariya zuwa Kano, direbobin tanka sun rufe hanyar don gudanar da zanga-zanga.

Da misalin karfe 3:30 na ranar Laraba ne dai wani soja da ke aiki a wani kamfanin gini ya harbe direban har lahira bayan sun samu sabani a Tashar Yari da ke Makarfi, kusa da babbar hanyar.

Duk kokarin da ’yan sanda da Kungiyar Ma’aikatan Sufuri (NURTW) na bude hanyar tun a ranar Laraba ya ci tura, direbobin tankar sun ki janye motocinsu.

Kwamandan Hukumar kiyaye Haddura na shiyyar, Lawal Garba, ya ce duk da ba su gano musabbabin zanga-zangar ba, bincikensu ya tabbatar da an harbe direban tankar.

“Wannan lamari dai  bai yi dadi ba, domin tun ranar Laraba abu ya ki ci, ya ki cinyewa; mutane na shan wahala sakamakon hakan”, a cewarsa.

Sai dai ya ce hukumar na ci gaba da kokarin shawo kan lamarin, da taimakon sauran masu ruwa da tsaki.