✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direbobin tanka sun toshe hanyar Zariya-Kano bayan kashe daya daga cikinsu

Sai da jami’an tsaro suka sa baki kafin a bude hanyar

Direbobin tanka sun toshe babbar hanyar Zariya zuwa Kano a ranar Laraba, don nuna bacin ransu kan kisan daya daga cikinsu da suke zargin wani soja da yi.

Lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 3:30 na yamma, lokacin da direbobin suka haddasa mummunan cunkoson ababen hawa sakamakon rufe hanyar na tsawon sa’o’i.

Aminiya ba ta kai ga tantance abin da ya kai har sojan, wanda ke aiki tare da wani kamfanin gine-gine, ya kashe diren ba.

Sai dai bayanai sun nuna lamarin ya faru ne a kusa da garin Tashar Yari da ke Karamar Hukumar Makarfi ta Jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da tare hanyar, da ma kisan direban, mai rikon mukamin Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Kaduna, Lawal Garba, ya ce sai da aka yi amfani da sauran jami’an tsaro kafin a bude hanyar ga sauran masu wucewa.

Ya ce, “Toshe hanyar ya fara ne bayan wani soja da ke aiki da kamfanin da ke aikin gina titi ya harbe direban saboda wata tankiya da ta auku a tsakaninsu.

“Hakan ce ta sa direbobin tankar suka toshe hanyar baki daya don nuna fushinsu.

“Na kira Daraktan DSS da Kwamishinan ’Yan Sanda da kuma Daraktan Tsaron Cikin Gida a kan lamarin. Yanzu haka muna kokarin shawo kan lamarin,” in ji shi.

Aminiya ta gano cewa tuni wanda ake tuhuma da aika-aikar ya fada hannun sojoji.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya ce tuni Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar, Yekini Ayoku, ya ba da umarnin zurfafa bincike a kan lamarin.