✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direbobin Tanka sun toshe wata babbar hanya a Lokoja

Gwamnan ya kuma bayyana rashin jin dadinsa kan mutuwar direban.

Kungiyar direbobin tanka sun hana zirga-zirga a titin Abuja zuwa Lokoja a daren ranar Litinin saboda mutuwar daya daga cikinsu da ya ki tsayawa a shingen binciken tsaron soji, da ke Jamata a  kusa da gadar Murtala Muhammad.

Wata majiya ta bayyana cewa direban ya ki tsayawa bayan sojojin da ke aiki a shingen sun dakatar da shi, kuma suka bi shi bayan ya ki tsayawar.

Majiyar ta kuma ce bayan lura da sojojin na biye da shi ne, ya sanya ya tsayar da motar ya tsere daji in da ya fada wani rami ya kuma samu munanan raunuka.

An dai gaggauta kai shi asibiti, kafin daga bisani rai ya yi masa halinsa.

Mutuwar ta sa dai ita ce ta janyo bacin ran direbobin tankar, in da suka toshe babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja.

A hannu guda kuma Gwamnan Kogi Yahaya Bello a ranar Talata ya ba da umarnin gaggauta bude hanyar ta bakin hadiminsa na musamman kan sha’anin tsaro, Mista Omodara Jerry.

Gwamnan ya kuma bayyana rashin jin dadinsa kan mutuwar direban, sai dai ya yi Allah wadai da abinda direbobin tankar suka aikata da sunan huce takaici.

Ya ce akwai hanyoyin da kungiyar za ta nuna bacin ranta, amma ba ta takurawa al’ummar da ba su ji ba ba su gani ba.

Haka kuma ya ce hanyar Abujan na da matukar muhimmacin da gwamnati ba za ta zuba ido a rufe ta ba, domin zai kawo cikas ga kasuwanci da rayukan al’umma.