✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dogara ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC

An sanar da sauya shekarsa daga PDP ne bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sanar da haka bayan ganawar shi da Dogara suka yi da Shugaba Buhari a ranar Juma’a.

Buni shi ne shugaban Kwamitin riko na jam’iyyar APC da ke jagorantar sasanta bangarorin jam’iyyar da ke rikicin shugabanci.

Kafin zamansa gwamnna shi ne tsohon Sakataren Jam’iyyar da ya jagoranci sulhu tsakanin bangarorin jam’iyyar a baya.

Dogara na daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar APC da suka fice daga cikinta zuwa tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP, gabanin zaben 2019.

Kari na tafe…