✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dogaran fadar Shehun Borno 3 sun kone kurmus a hatsarin mota

Hatsarin ya faru ne lokacin da motar ta kama da wuta.

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), ta tabbatar da rasuwar wasu Dogaran Fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Ibn Garbai El-kenmi, a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a hatsarin mota.

Kwamandan hukumar a jihar, Utten Iki Boyi ne, ya shaida wa Aminiya a Maiduguri a safiyar ranar Talata cewa mutum shida ne suka yi hatsarin wanda ya auku a ranar Litinin, amma an ceto uku inda aka mika su wani asibiti don ba su agajin da ya kamata.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a kusa da yankin Benisheik a lokacin da motar ta kama da wuta.

“Nan da nan muka samu rahoton, tawagarmu ta garzaya wurin da lamarin ya faru. Mutane uku sun kone kuma ba za a iya gane su ba. Sai dai kuma an kubutar da mutane uku kuma an kai su babban asibitin Benishiek domin yi musu magani.

“Zan iya tabbatar muku da cewa mutum uku sun rasa rayukansu,” in ji shi.

An ruwaito cewar cewa fasinjoji ukun da suka kone, ma’aikatan Shehun Borno ne yayin da wasu uku suka tsira da raunuka a jikinsu.