✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar hana cin naman shanu na nan daram a Kudu – IPOB

IPOB ta ce ba gudu ba ja da baya a kan dokar hana shanu zirga-zirga a yankin.

Kungiyar ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), ta jadadda dokar hana zirga-zirgar shanu don yin kiwo a yankin Kudu Maso Gabas tare da hana cin naman shanun Fulani daga watan Afrilu mai zuwa.

Kungiyar dai ta kuduri niyyar yakar mutanen yankin daga samun tasirin Fulani a rayuwarsu ta yau da kullum.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful, ya fitar a ranar Litinin cewar yankin na kashe sama da biliyan uku duk shekara wajen cin naman shanu wanda ya ce dole ne su kawo karshen hakan.

IPOB ta jadadda cewar duk masu ta’ammali da naman shanu su nema wa kansu mafita kafin kamawar watan Afrilu.

“Muna son jadadda cewar dokar hana zirga-zirgar shanu a kasar Biyafara tana nan daram, kuma za ta fara cikakken aiki daga watan Afrilu.

“Muna jan hankali cewar duk wasu bayanai da ke yawo a kan wannan doka ba gaskiya bane, doka na nan daram, ba gudu ba ja da baya.

“Tun farko mun amince tare da daukar mataki kan irin kisan-gillar da Fulani ke yi mana, sannan da gaza yin katabus daga jami’an tsaron Najeriya,” cewar sanarwar.

IPOB dai ta sha kafa dokar zaman gida a Kudu Maso Gabas, tare da kai hare-hare a kan Fulani ko dabobbinsu, lamarin da ya janyo asarar dukiyoyi masu tarin yawa da kuma salwantar rayuka.