✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dokar kasa ta halasta shugabancin kwamitinmu —APC

Kwamitin rikon jam’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya ce tsarin mulkin Najeriya da ya haramta gwamna mai ci rike wani mukami…

Kwamitin rikon jam’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya ce tsarin mulkin Najeriya da ya haramta gwamna mai ci rike wani mukami na albashi bai shafi kwamitin jagorancin jam’iyyar ba, tunda na riko ne.

Karo na farko ke nan da APC ta fito ta yi magana kan lamarin bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanka a kan shari’ar zaben Gwamnan Jihar Ondo, wanda kotun ta tabbatar da dan takarar jam’iyyar, Gwamna Rotimi Akeredolu, a matsayin wanda ya lashe zaben.

Daya daga cikin ’yan kwamitin, Farfesa Tahir Mamman, ya shaida wa ’yan jarida a hedikwatar jam’iyyar ta kasa a Abuja a ranar Laraba cewa jam’iyyar ta jinkirta bayaninta a kan lamarin ne har sai Kotun ta fitar da cikakken bayani a kan hukuncin da ta yanke.

Farfesa Tahir Mamamn ya gabatar da kwafin hukuncin ga ’yan jarida da cewa, “Kotun ta yanke hukuncin cewa, a  dokar kasa kwamitinmu bai da matsala saboda bai shafi mai rike da mukamin jam’iayya a matakin wucin gadi ba.

“Kotun ta ce jam’iyya na da hurumin nada kwamiti, sannan mas’ala irin wannan lamari ne na cikin gida da ba ta da hurumi a kai, kuma bai kamata wani ya gabatar da korafi ga kotu a kai ba,” inji shi.

A game da harkokin cikin gidan jam’iyyar, Farfesa Mamman Tahir ya ce a baya wasu fusatattun ’yan jam’iyyar adawa ta PDP sun shigar da kara lokaci da tsohon Gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sherif, ya rike jam’iyyar, inda a karshe Kotun ta nuna cewa mas’ala ce ta cikin gida, inji shi.

Jam’iyyar ta ce da wannan hukuncin, tana kira ga ’ya’yanta da ke da kara ko korafi a kan lamarin da su janye.

“Sannan su fahimci cewa lamarin jam’iyya ba na kotu ba ne, saboda yana kawo koma baya; Lamari ne na tattaunawa da kuma fahimtar juna,” inji jam’iyyar.

Taron ya samu halarcin sakataren kwamitin rikon, Sanata Sanata Akpan Udoedehe da Hadimin Shugaban Kasa kan al’amuran Tallafi, Basrista Ismaila Ahmed, sai kuma Babban Haidimin Shugaban kwamitin jam’iyya, Alhaji Abdullahi Yusuf.