✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar Kulle: El-Rufa’i ya jinjina wa Musulmin Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya jinjina wa Musulmin jihar Kaduna bisa juriya da hakurinsu a lokacin azumin watan Ramadan wanda aka yi cikin…

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya jinjina wa Musulmin jihar Kaduna bisa juriya da hakurinsu a lokacin azumin watan Ramadan wanda aka yi cikin dokar kulle a jihar.

El-rufa’i ya shaida haka ne a sakon gaisuwar sallahd ya aike wa al’ummar Musulmi wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

“Gwamna Nasir El-Rufai na taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin Ramadan a cikin wannan mawuyacin yanayi.

“Ya yaba da juriya da fahimtar da suka nuna yayin gudanar da ayyukan ibada a cikin yanayin dokar hana fita,” inji sanarwa.

A jihar Kaduna an gudanar da azumin watan Ramadan da sallar idi a cikin dokar kulle da gwamna Nasir El-Rufa’i ya ayyana a kokarinsa na kare yaduwar annobar coronavirus.