✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar mai: Majalisa za ta yi mahawara 20 ga Oktoba

Majalisa za ta kammala mahawara da karatu na biyu a kan dokar man fetur kafin ta fara aikin kasafin 2021

Majalisar Dattawa za ta fara muhawara a kan Kudurin Dokar Man Fetur (PIB) da Shugaba Muhammadu Buhari ya aike mata mako uku da suka gabata.

Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan ya ce za a yi mahawarar ne a ranar Talata ga watan Oktoba 2020, domin kauce wa jinkiri sakamakon kammala aiki a kan kasafin 2021.

“Za mu mika PIB ga Kwamitin Hadin Gwiwa kafin dakatar da zaman zauren majalisa saboda kar kudurin zai yi ta zama ba a kula shi ba a tsawon lokacin aikin kasafin kudin.

“Idan ba haka ba, to ba za mu fara aiki a kai ba sai lokacin mun dawo a watan Nuwamba ko Disamba kuma lokaci ya kure.

“Na san kowa na jiran a yi PIB amma za mu dauki issasshen lokaci mu yi aiki a kai saboda tana da matukar tasiri.

“Duk da haka a Talata 20 ga Oktoba, 2020, za mu yi mahawara da karatu na biyu a kanta sannan mu mika wa Kwamitin Albarkatun Mai da Iskar Gas na Majalisar Tarayya”, inji shi.

Bayanin nasa a zaman majalisar na ranar Alhamis bayan Shugaba Buhari ya gabatar da daftarin kasafin 2021, ya ce za a yi mahawarar ne lura da dakatar da zama na wata guda da majalisar za ta yi domin sauraron kare kasafin 2021 na hukumin gwamanti.

“Yayin da muke aikin kasafin, kwmaitocin za su rika aiki a kan kudurin dokar.

“Ba za mu yi sauri ba saboda aikin kasafin kudi da ke gabanmu.

“Kwamitin zai kammala aiki a kan kudurin ya shirya rahoto ko kundi da Majalisa za ta yi aiki da shi wanda ‘yan Najeriya da masu zuba jari su yi na’am da shi”, kamar yadda ya ce.