✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dokar NCDC: Takaddama ta barke tsakanin majalisa da gwamnoni

Majalissar Wakilai ta Najeriya ta soki matsayin da gwamnonin kasar suka dauka a kan kudurin dokar dakile cututtuka masu saurin yaduwa. Gwamnonin dai sun yi…

Majalissar Wakilai ta Najeriya ta soki matsayin da gwamnonin kasar suka dauka a kan kudurin dokar dakile cututtuka masu saurin yaduwa.

Gwamnonin dai sun yi kira ga majalisar ne a kan ta dakatar da muhawara a kan kudurin dokar wanda aka yi wa taken “Kudurin Dokar Dakile Cututtuka Masu Saurin Yaduwa na 2020” a cikin wata takardar bayan taro da suka fitar bayan kammala taron Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF).

A cikin wata takardar martani da ta fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ta, Benjamin Okezie Kalu, majalisar ta ce ita fa ba ta yi wa jihohi dokoki, saboda haka matsayin gwamnonin a kan kudurin dokar bai da tushe.

“Majalisa ta samu labari cewa Kungiyar Gwamnoni ta fitar da sanarwa bayan taron da ta gudanar ta intanet ranar Laraba, 13 ga watan Mayu na Shekarar 2020, tana yin kira ga Majalisa ta dakatar da zartar da ‘Kudurin Dokar Dakile Cututtuka Masu Saurin Yaduwa na 2020’ wanda tuni aka yi shirin gudanar da zaman jin bahasin jama’a a kai.

‘Ba mu yarda da matsayin Tambuwal ba’

“A cikin takardar bayan taron, gwamnonin sun ce ‘Bayan samun bayanai a kan Kudurin Dokar Dakile Cututtuka Masu Saurin Yaduwa na 2020 na Majalisar Wakilai daga Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kungiyar, gwamnoni sun nuna damuwar su a kan rashin tuntubar su duk da cewa su ne abin yafi shafa’”.

Takardar martanin ta ci gaba da cewa, korafin gwamnonin ya zo a makare domin a zamanta na wannan makon, Majalisar ta yanke shawarar gudanar da zaman jin ra’ayin jama’a a kan kudurin dokar domin ta bai wa ’yan Najeriya damar tofa albarkacin bakin su.

“Majalisa tana so ta jaddada cewa bayan cewa aikin ta ne ta yi dokoki ga Jamhuriyar Najeriya, kuma ita ce Majalisar Babban Birnin Tarayya, duk da haka ’yan Majalissar suna daukar Kungiyar Gwamnonin a matsayin jagora a fannin ginawa da ciyar da kasa gaba.

“Abin mamaki ne a ce NGF ta dauki matakin ne bisa dogaro da ‘abin da gwamnan Sakkwato ya gabatar mata’ wanda bayan kasancewar sa lauya, tsohon Kakakin Majalisa ne kuma tsohon dadadden dan majalisa, wanda kuma ya kamata a ce ya san me doka ta ce.

“Muna tsammanin cewa ya dauki wannan matsayin ne ta fuskar zaman sa na wanda yake adawa da shugabancin Majalisar da muke da shi a yanzu idan aka yi la’akari da matsayin sa a shekarar 2015 da kuma 2019”, inji takardar.

‘Majalisar Tarayya na cin gashin kanta’

Majalisar ta kara da cewa sabanin abin da ya shafi gyaran Kundin Tsarin Mulki na kasa wanda majalisun dokokin jihohi suke da rawar da za su taka, kudurorin doka kamar Kudurin Dokar Dakile Cututtuka Masu Saurin Yaduwa na 2020 ba sai su ko gwamnonin sun saka baki ko an tuntube su ba.

Ta kuma sake jaddada cewa Majalisar Wakilai da ma Majalisar Tarayya gaba daya suna cin gashin kansu ne, ba a karkashin gwamnonin jihohi ko wani tsohon Kakakin Majalisa ba.

Majalisar ta ce idan gwamnonin suna so a canza tsarin, sai ta hanyar gyaran dokokin kasa wanda ’yan kasa za su nema ba domin ra’ayin wani gwamna ko tsohon Kakakin Majalisa ba.

“Amma duk da haka, Majalisa tana shirye ta yi aiki da kwamitin da Kungiyar Gwamnonin ta kafa domin su hadu da mambobin Majalisa a kan dokar.

“Gwamnonin suna da muhimmanci a ginawa da ci gaban kasa, kuma mun fahimci amfanin su a wannan lokacin da muke fuskantar annoba.

“Majalisa tana sane da cewa Kungiyar Gwamnonin tana da damar daukar matsayi a kan duk wani kudurin doka, ta rubuto lokacin da za a yi zaman jin bahasin jama’a wanda ake shirin yi, ko kuma ta turo wakilai lokacin da za a yi.

“Har yanzu babu wani gwamna da ya tuntubi Kakakin Majalisa ko wani daga cikin shugabannin ta domin ya fadi wani ra’ayinsa.

‘NGF ta yi kuskure’

“Abin da muka yarda da shi shi ne, akwai kafofin sadarwa da yawa wadanda NGF za ta iya amfani da su don tuntubar Shugabancin Majalisar ba shafukan jaridu ba.

“Majalisa tana da shakku a kan kasancewar Gwamnan Sakkwato a cikin Kwamitin Tuntuba na NGF domin ba zai bari a samu kayakkyawar fahimta ba, domin a matsayin sa na tsohon Kakakin Majalisa, bai iya fahimtar da kungiyar yadda ya kamata ba a kan kudurin dokar.

“Sannan kuma ya dauki wani matsayi na son ran sa”, inji sanarwar Majalisar.