✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dokar taron ibada: An ci tarar limaman Juma’a biyu a Bauchi

Wata kotun tafi-da-gidanka a Bauchi ta yanke wa wasu limamai biyu hukuncin biyan tara ta N20,000 ko wanne, bayan ta same su da laifin jagorantar…

Wata kotun tafi-da-gidanka a Bauchi ta yanke wa wasu limamai biyu hukuncin biyan tara ta N20,000 ko wanne, bayan ta same su da laifin jagorantar sallar Juma’a a masallatai daban-daban.

An gurfanar da limaman, Malam Musa Hassan da Malam Dahiru Alhaji, a gaban kotun ne ana tuhumar su da yin karan tsaye ga dokar gwamnatin jihar ta hana taruwa a wuraren ibada.

Duk su biyun dai a kauyen Dunkui Ambi na karamar hukumar Misau suke.

Kotun, a karkashin jagorancin Alkalin Majitare Muktar Abubakar, ta ce ba za ta yi wa duk wanda aka samu yana saba wa dokar jihar ta hana wasu harkoki da sauki ba.

Alkali Abubakar ya yi kira ga al’ummar jihar su yi biyayya ga umarnin hukumomi.

A yanzu haka dai gwamnatin jihar ta Bauchi ta haramta tarukan jama’a, ciki har da taruka a wuraren ibada, a yunkurin hana kwayar cutar coronavirus yaduwa.