✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole a hukunta Saraki da Abdulfatah kan almundahana —Gwamnan Kwara

Gwamnan ya ce ba sani ba sabo ga duk wanda aka kama da laifi.

Gwamnan Kwara Abdulrahman Abdulrazaq, ya ce dole ne a hukunta tsoffin Gwamnonin jihar biyu, Bukola Saraki da Abdulfatah Ahmed saboda karya da suka yi wurin bayyana kadarorinsu.

Hakan na zuwa ne bayan Saraki ya musanta zargin da ake masa na yin ruf da ciki a kan kudaden jihar lokacin da ya ke Gwamna.

Gwamnatin Kwara na zargin Saraki wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattijai ne da gaza cika alkawuran da ya dauka na yakin neman zabe.

Sai dai Gwamnan, ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, ya yi tir da zarge-zargen da PDP ke masa, inda ya ce rashin sanin makamar mulki ne ya sa jam’iyyar adawar take neman laifi a inda babu shi.

“Binciken da muka gudanar ya gano yadda gwamnatin baya da wasu jami’anta suka yi sama-da-fadi da dukiyar al’umma duk da yardar da jama’a suka amince musu.

“Muna ba da tabbacin cewa duk wanda rahoton kwamiti ya ba da cikakkiyar hujja a kansa, zai fuskanci hukunci,” kamar yadda Gwamnan ya bayyana.

Ya ce gwamnatinsa a shirye take ta karbi kowanne irin gyara ko tsokaci da zai taimaka wajen inganta jihar.

Abdulrazaq ya bugi kirjin cewa gwamnatinsa ita ce mafi aiki da aka taba yi tun kafuwar jihar.