✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole a kara kasafin kudin Najeriya – Bagudu

Gwamnan ya ce gwamnatin jam'iyyarsu na sane da kalubalen da kasar nan ke fuskanta.

Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya ce dole ne a kara kasafin kudin Najeriya zuwa tsakanin Dalar Amurka biliyan 300 zuwa 500, domin shawo kan kalubale da dama da suka yi wa kasar kaka-gida.

Ya fadi hakan a Abuja a karshen mako yayin kaddamar da wani littafi da ke magana kan kamun ludayin APC a Dimokoradiyyar Najeriya da siyasar canji, wanda Darakta Janar na Kungiyar Gwamnonin Jamíyyar APC, Salihu Mohammed Lukman ya wallafa.

Gwamnan, wanda kuma shine shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, ya ce gwamnatin jam’iyyarsu na sane da kalubalen da kasar nan ke fuskanta da ke bukatar a shawo kansu.

A cewar Bagudu, “Idan wani ya kwatanta kasafin kudin Najeriya da na Amurka, kasar da ke da yawan al’umma miliyan 331, za ka ga a 2019, kasafin kudin Amurkar ya fi Dala tiriliyan 3.5, kashi daya na wadannan kudaden shi ne Dala biliyan 35.

“Hakan ya nuna kasafin kudinmu, yana kasa da nasu. Sannan a wani gefen muna da al’ummar da ta kai kimanin kashi 70 na yawan al’ummar Amurkar.

“Idan kuma ka yi la’akari da rabon arzikin kasa da ake yi wata-wata, zai kara fayyace maka lamarin.

“Alal misali, daga watan Janairu zuwan Mayun bana, a dukkanin taron Majalisar Rabon Arzikin Kasa, babu wani watan da aka taru aka raba Dala biliyan biyu.

“Don haka, idan lamarin ya dore a haka yana nuna cewa matakan gwamnati uku za su taru su raba Dala biliyan biyu a kowane wata kenan.

“Wannan shi ne babban kalubalen da ya kamata mu sanar wa jama’a; sannan Shugaba Muhammadu Buhari ya ladabtar da mu tare da gwada mana darajar alkinta kudi.

“Amma yanzu muna cikin yanayin da dole mu kara fadada hanyoyin samun kudi domin ganin mun kara kasafin kudin tarayya daga Dala biliyan 35 zuwa 300 ko 500, har sai mun yi hakan ne kawai za mu iya cimma tarin bukatunmu a dukkanin bangarorin rayuwa,” inji Gwamna Bagudu.