✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole ce ta sa makiyaya suka fara amfani da AK-47 –Gwamnan Bauchi

“Muna da Yarbawa a Bauchi sama da shekaru 150, tun ma kafin a kirkiri Najeriya.”

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ce tilas ce ta sa Fulani makiyaya daukar makamai domin su kare kansu.

Gwamnan, wanda ke wadannan kalaman yayin Bikin Makon Wakilan Kafafen Watsa Labarai na Kungiyar ’Yan Jaridu ta Kasa (NUJ) reshen jihar Bauchi, ya kuma ce sun fara daukar makaman ne da nufin kare kansu daga barayin shanu.

Ya zargi gazawar gwamnati wajen kare Fulanin da cewa ita ce ummul-aba’isun da ta sa suka fara daukar makamai domin su kare kansu.

A cewarsa, “Saboda dan Fulani yana yawon kiwo, hakan ya sa ya fara cin karo da barayin shanu wadanda ke dauke da bindigogi, su kashe shi sannan su raba shi da arzikinsa, wato shanunsa.

“Hakan ce ta sa ya yanke shawarar daukar AK-47 saboda al’umma da ma gwmanati sun kasa tare shi. Mene ne laifinsa? Laifin gwamnati ne da na sauran al’umma.

“Ba daidai ba ne a yi wa dukkan Fulani kudin goro, a cikin kowacce kabila akwai baragurbi.”

Gwamna Ortom na kokarin bata sunan Fulani

Kazalika, Gwamnan ya kuma zargi takwaransa na jihar Binuwai, Samuel Ortom da kokarin bata sunan ilahirin Fulani a kafafen watsa labarai.

Hakan, a cewarsa ya kara rura wutar rikicin makiyaya da manoma.

“Gwamnan da ya fi kowanne kaurin suna a wannan fagen shine takwarana na jihar Binuwai, Samuel Ortom; shine duk ya fara wannan abin.

“Idan ba ka rungumar sauran kabilu, ya kamata ka sani cewa mu muna rungumar naka a Bauchi da ma sauran jihohi.

“Muna da ’yan kabilar Tibi da yawa da suke noma a Kananan Hukumomin Alkaleri da Tafawa Balewa da Bogoro, akwai wanda ya taba ce musu su bar yankunan?

“Ba mu taba ba, saboda suna da ’yancin zama a wuraren.

“Muna da Yarbawa a Bauchi sama da shekaru 150, tun ma kafin a kirkiri Najeriya. Wadansunsu sun ma rike manyan mukamai kamar na Manyan Sakatarori a Bauchi da Gombe da Borno.

“Amma ku duba abin takaicin da takwarorinmu gwamnonin Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas suke yi.

“Idan har ’yan kabila daya za su yi kaurin suna wajen zamba ta intanet, hakan bai kamata ya sa a yi wa dukkan ’yan kabilar kudin goro cewa halinsu daya ba,” inji Gwaman Bala.