✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole mulki ya dawo yankinmu a 2023 – Gwamnonin Kudu

Gwamnonin sun kuma yi fatali da bukatar basu kaso uku cikin 100 na arzikin mai.

Gwamnonin Kudancin Najeriya sun ce dole ne mulki ya koma yankinsu a shekarar 2023 idan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa na biyu.

Gwamnonin sun bayyana hakan ne yayin wani taro da suka gudanar a Legas ranar Litinin, inda suka ce wanan ita ce yarjejeniyar da aka cimma.

Gwamnonin sun kuma yi fatali da bukatar basu kaso uku cikin 100 na arzikin man fetur kamar yadda sabon Kudirin Dokar Man da Majalisar Dokoki ta kasa ta amince a kwanan nan, inda suka ce baza ta dabu ba.

A maimakon haka, sun bukaci a rika basu kaso biyar cikin 100 kamar yadda Majalisar Wakilai ta bukata.

A ranar Alhamis ne dai Majalisar Dattijai ta amince da kudirin dokar man fetur din bayan shafe kusan shekara 20 yan fuskantar cikas.

A cewarsu, “Ba za mu yarda a rika bamu kaso uku cikin 100 na arzikin man fetur ba, sai dai kaso biyar kamar yadda Majalisar Wakilai ta bukata.

“Kazalika, ba za mu amince da bukatar bamu kaso 30 cikin 100 na ribar danyen mai da iskar gas din da ake haka a yankunanmu ba.

“Ba zamu lamunci da yadda aka sauya fasalin Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ba. Ba zamu yada ace kamfanin ya koma karkashin Ma’aikatar Kudi ba, sai dai karkashin Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIA), tun da dai dukkan matakan gwamnati uku na da ruwa da tsaki a tafiyar da shi.

A kan matsalar tsaro kuwa, Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya ce takwarorin nasa sun amince da ranar 21 ga watan Satumba a matsayin rana ta karshe ta nuna rashin amincewarsu da yin kiwo a yankin.

Gwamnan ya ce tuni aka ba jami’an tsaron yankin umarnin su nemi izini daga Gwamnonin Jihohinsu kafin daukar kowanne irin mataki.

To sai dai Gwamnan bai ce uffan game da kamun da aka yi wa shugaban kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu da kuma dirar mikiyar da jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS suka yi a gidan Sunday Igboho ba.