✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole sai mun yi sulhu da ’yan bindiga za a samu zaman lafiya — Matawalle

Amma hakan ba ya nufin kada mu ki yakar wadanda suka ki rungumar tsarin sulhu.

Gwamna Muhammad Bello Matawalle na Jihar Zamfara, ya sake nanata cewa sulhu da ’yan bindiga ita kadai ce hanya mafi a’ala da za a samu zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.

Matawallen Maradun ya bayyana hakan wata hira da ya yi yayin amsa tambayoyin manema labarai ranar Alhamis a Yola, babban birnin Jihar Adamawa.

Aminiya ta samu cewa Gwamnan ya kai ziyarar aiki Jihar Adamawa ne domin halatar bikin kaddamar da wasu ayyuka na gina tituna a yankunan karkara da kuma rarraba wasu ayyukan gyare-gyare da aka gudanar a Kuva-Gaya da ke Karamar Hukumar Hong ta Jihar.

A cewarsa, mafi kyawun zabin da zai kawo karshen tashin-tashina da kuma kawon karshen ta’addancin ’yan bindiga a Zamfara da sauran yankuna shi ne a tattauna domin yin sulhu da su.

“Na sha fadin cewa, mafificiyar hanyar da za a kawo karshen ta’addanci shi ne yin sulhu da ’yan bindiga.”

“Idan har muna son ganin bayan wannan ta’addanci, ya zama wajibi mu zauna da su a kan teburin sulhu.”

“Saboda ta hanyar sulhu da tattaunawa da muka rika yi mun samu nasarar kubutar da mutane da dama da aka yi garkuwa da su.”

“Don haka, mafificiyar hanya ga sauran takwarorina gwamnoni ita su rungumi tsarin tattaunawa domin yin sulhu da ’yan bindiga,” in ji Matawalle.

Gwamnan ya nanata cewa, rungumar tsarin zama a teburin sulhu da ’yan bindigar ba ta nufin kada a yaki wadanda suka ki tuba, sai dai gwamnati na amfani da dabaru da dama domin ganin hakarta ta cimma ruwa wajen samun zaman lafiya mai dorewa.

Kazalika, ya ce ’yan bindigar da suka nemi a yi sulhu, gwamnati tana zama tare da su domin sauraron korafe-korafe da abubuwan da suka fusata su.

Sai dai duk dan ta’addan da bay a niyyar tuba ko rungumar tsarin sulhu, to zamu yake shi, don a matsayina na Gwamna, nauyi na farko da ya rataya a wuyana shi ne tabbatar sa zaman lafiya mai dorewa domin al’umma su yi bacci har da munshari,” inji Matawalle.