✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole sojoji su yi bayani kan kudaden da suke kashewa a harkar tsaro —Osinbajo

Ya dace a ce Najeriya ta shawo kan matsalar ’yan bindigar da ake fama da ita.

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bukaci sojojin kasar da su yi wa jama’a bayani akan irin makudan kudaden da gwamnati ta basu domin gudanar da ayyukan tsaro a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.

Osinbajo ya ce akwai bukatar sojojin kasar su yi bayani dalla-dalla yadda suke kashe kudade wajen sayo makamai da kayayyakin aiki domin magance matsalar tsaro.

Mataimakin Shugaban Kasar ya ce jama’ar kasa na da hurumin sanin irin makudan kudaden da wannan gwamnati ta ware domin tunkarar matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

Babu shakka matsalar tsaro ta janyo asarar dubban rayuka da dukiyoyi, lamarin da Mataimakin Shugaban Kasar ya nemi sojiji da su kore shakku dangane da yadda gwamnati ke fuskantar kalubalen tsaron.

Farfesa Osinbajo ya ce abin takaici ne kowane lokaci idan an yi maganar tsaro, sai kaji wasu sojojin na cewa basu da kayan aiki, saboda haka ya dace ma’aikatar tsaro ta gabatar da wani tsari wanda zai dinga bayyana irin kudaden da su ke kashewa a bangaren tsaro.

Osinbajo ya bayyana cewar ya dace a ce Najeriya ta shawo kan matsalar ’yan bindigar da ake fama da ita ta wajen nuna kwarewa da kuma nuna dabarun yaki.

Aminiya ta waiwayi kasafin kudin tsaron da aka bai wa Ma’aikatar Tsaro tun shigowar gwamnatin Buhari a shekarar 2015 zuwa yanzu kamar haka:

2015 – Naira biliyan 968

2016 – Naira Triliyan guda da miliyan 700

2017 – Naira Triliyan guda da miliyan dubu 1 da 500

2018 – Naira Triliyan guda da miliyan dubu 1 da 350

2019 – Naira Triliyan guda da miliyan dubu 1 da 400

2020 – Naira Triliyan guda da miliyan dubu 800

2021- Naira Triliyan guda da miliyan dubu 960 da kuma kasafi na musamman Naira biliyan 722 da miliyan 530.