✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole su Amaechi da Ngige su ajiye aiki cikin kwana 5 —Buhari

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta umarci duk mambobinta da ke son yin takara a 2023 su ajiye aiki zuwa ranar 16 ga Mayu, 2022

Majalisar Zartarwa ta Tarayya, ta umarci Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da sauran ministocin da ke zawarcin kujerar shugaban kasa a zaben 2023 su ajiye mukamansu nan da ranar 16 ga watan Mayun da muke ciki.

Minsitan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, shi ne ya sanar da hakan bayan zaman Malisar Zartawar ta Tarayyar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagornta ranar Laraba a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Umarnin ya shafi duk wani mamba a Majalisar Zartarwa ta Tarayya da ke neman takara a zaben 2023, ciki har da Ministan Kwadago da Kyautatuwar Aiki, Chris Ngige.

Sauran su ne Minista a Ma’aikatar Ilimi, Emeka Nwajiuba; da Minista a Ma’aikatar Mai, Timipre Sylva, masu neman takarar shguaban kasa.

A kwai kuma Ministan Kimiyya da Fasa, Ogbonnaya Onu da kuma Ministan shari’a Abubakar Malami da ke neman takarar Gwamnan Jihar Kebbi.

Karin bayani na tafe…