✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Don ma’aurata: Bayani kan soyayya…

Bayani game da ilimin soyayya, dabbaka ta da alkinta ta cikin huldodi da zamantakewar aure.

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

Za mu fara gabatar da bayani ga ma’aurata game da ilimin soyayya da yaya za su dabbaka, su alkinta soyayya cikin huldodinsu da zamantakewar aurensu:

 

Ma’anar soyayya:

Kalmar soyayya tana nufin samuwar kyawawan shau’ukan so, kauna da fatar alheri cikin zuciya, wadanda za a bayyanar da su a aikace ta hanyar nuna kula da kyautatawa da tausayawa ga wanda ake son, da kuma kokarin samar da jin dadi da farin ciki; da kore bakin ciki da wahala.

Soyayyar auratayya kuwa ita ce dunkulalliya kuma cikakkiyar kulawar ma’aurata ga junansu ta hanyar samar da wadancan abubuwa da aka ambata a sama.

Daga wannan bayanin muna iya fahimtar cewa soyayya wata itaciya ce mai rassa biyu muhimmai:

Reshen farko na dauke da kyawawan shau’uka cikin zuciya a badinance, reshe na biyu na dauke da aiwatar da wadannan shau’uka a zahirance.

 

’Ya’yan tsiron soyayya

Wadannan su ne abubuwan da suke tsirar da shaukin soyayya cikin zuciya, kowanensu na da muhimmanci wajen tallabar soyayya.

Sannan irin yanayin inganci da karfin tsiron, irin yanayin sakamakon soyayyar da za ta bayyana; in kuma tsiron ya samu nakasu, to zai haifar da nakasu ga soyayyar da ya tsirar.

Tsiro daya na iya tallafar soyayya har ta kammala matukar bai samu nakasu ba, amma da ya samu nakasu, to zai yiwu ma a nemi soyayyar a rasa.

Don haka kammalalliyar soyayya, wacce ke iya jure kowane irin yanayi, ita ce wacce take kunshe da dukkan ’ya’yan tsiron nan da bayaninsu zai zo:

1. Kauna

Kauna ita ce tsiron farko da ke haifar da soyayya, kuma ta kasance tsabtatacciyar shauki ne da ya samo asali bisa wani dalili tsabtatacce kuma abin burgewa ga zuciyar da take kaunar.

 

Kauna ta kasu gida biyu:

Tabbatacciyar kauna

Ita ce wacce ba ta taba daukewa daga cikin zuciya komai daren dadewa.

Wannan ita ce irin kaunar da muke yi wa ’ya’yanmu, iyayenmu da ’yan uwanmu.

Komai ya faru na yanayin rayuwa, bai iya tumbuke tsiron kaunar gaba daya daga cikin zuciya.

Tabbatacciyar kaunar da ta yi zarra a wannan bangare ita ce kaunar uwa ga danta, domin akwai yiwuwar kaunar iyaye da ’yan uwa ta ragu ko ta karu a dalilin faruwa ko rashin faruwar wani abu, amma kaunar uwa ga danta ba ta taba raguwa cikin zuciya.

 

Kauna marar tabbas

Ita ce kaunar da ta faru a bisa wani dalili mai canjawa: da zarar dalilin ya canja, to kaunar ma za ta canja ko ta dauke gaba daya; wadannan sun kunshi:

Mallaka: Mallakar wani abu mai kyau kuma mai alfanu ga mutum na tsirar da kaunar abin nan cikin zuciya; wannan ne ya sa muke kaunar ma’auranmu da dangi mafiya kusanci.

Kyautatawa/kulawa: Duk zuciya na kaunar mai kyautatawa gare ta, domin ita kyautatawa alama ce ta nuna kauna.

Kyan hali: Wata kaunar na tsira ce a dalilin kyan hali da irin yadda halin ya burge zuciya.

 

2. Sabo: Duk lokacin da mutum biyu suka saba da juna, kullum suna haduwa tare, ko suna yawan haduwa ko suna yawan aiwatar da wani abu tare, dole ne kaunar juna ta kullu a tsakaninsu.

Shi ma sabo, ya kasu kashi biyu ta yadda yake tsirar da soyayya, sabon da aka yi shi hade da fahimtar juna shi ke haifar da sahihiyar soyayya da mutunta juna, sabon da aka yi shi ba fahimtar juna, bai haifar da soyayya sai dai a ce masa sanayya kawai.

 

3. Tausayi:

Shi ma yana tsirar da soyayya cikin zuciya, in shaukin tausayi ya bayyana cikin zuciya to yana nannade da shaukin soyayya, duk wanda ake tausayi, to tabbas ana son sa.

 

4. Amincewa

Yarda da amincewa tsakanin mutum biyu na tsirar da soyayya da kaunar juna cikin zuciyarsu, haka kuma rashin yarda da rashin amincewa na tsirar da rashin soyayya.

 

5. Sha’awa

Sha’awa ta kasance tana tsirar da gawurtacciyar soyayya lokacin da take kan ganiyarta, domin tana samar da dukkan sauran kayan hadin soyayya, musamman kyawawan shau’ukan jin dadi da sha’awar saduwar auratayya.

Sai dai sha’awa shaukin bogi ne domin ba ta da tsawon rai cikin auratayya.

Don haka soyayyar da sha’awa ce ta tsirar da ita, to karar kwananta kusa yake sai in an tallafe ta da wasu daga cikin sauran kayan hadin soyayya.

 

6. Shakuwa

Wannan ita ce babban jigon soyayya, domin cikin shakuwa, akwai kaunar juna, akwai sabawa, kuma akwai yarda da amincewa, sannan kasancewar shakuwa cikin dangantakar ma’aurata, na tsirar da tabbatacciyar sha’awa a tsakaninsu.

Dukkan sauran ’ya’yan tsiron soyayya na iya samun nakasu a cikin zuciya a bisa wani dalili, kuma da sun samu nakasu, to soyayyar ma za ta samu nakasu.

Amma shakuwa tabbatacciya ce cikin zuciya har abada, ba a taba dawowa a ce babu wannan shakuwar.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.