✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Donald Trump ya kaddamar da takararsa ta sake neman Shugabancin Amurka

Ya kaddamar da takarar ce a jihar Florida da yammacin Talata

A yanzu dai ta tabbata tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben 2024 mai zuwa, bayan ya kaddamar da takarar tasa a birnin Florida da yammacin Talata.

Ya kaddamar da takarar ce a unguwar Mar-a-Lago da ke Floridar, mako daya bayan jam’iyyarsa ta Republican ta yi asarar wasu kujeru a Majalisar Kasar da dama a zaben tsakiyar wa’adin da ya gudana a kasar.

A yayin wani jawabinsa da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin, Trump, ya yi jawabi ga daruruwan magoya bayansa a wani dakin taro da aka kawata da hotunansa da kuma tutocin Amurka.

“Domin mu sake farfado da martabar Amurka, yau a wannan daren nake sanar da aniyata ta sake tsayawa takarar Shugabancin Amurka.

“Ina neman takarar ce saboda na yi amannar cewa duniya ba ta ga ainihin girman da kasarmu za ta iya kai wa ba.

“Za mu sake farfado da martabar Amurka,” inji tsohon Shugaban mai shekara 76 a duniya.

Tun da farko dai a ranar ta Talata, hadiman Trump din sun aike da wani daftari da ke kunshe da kwamitin da suka kira na yakin neman zaben Donald J. Trump a 2024 ga Hukumar Zaben Kasar.

Akwai dai abubuwa da dama a gaban Trump kafin ya sami damar zama dan takarar jam’iyyar tasa ta Republican a zaben da za a yi a 2024.

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum na kallon yunkurin tsohon Shugaban na kaddamar da takarar tasa tun da wuri a matsayin kandagarkin hana abokan hamayyarsa tunanin fitowa a jam’iyyar.

Daga cikin wadanda ake hasashen za su nemi takarar a jam’iyyar har da Gwamnan jihar Florida mai shekara 44 da kuma Mataimakin Trump lokacin yana Shugaban Kasa, Mike Pence mai shekara 63.

Sai dai Trump, wanda sau biyu Majalisar Dokokin Amurka na tsige shi a zamanin mulkinsa, ya shiga takarar ce a lokacin da kasar ke fama da rashin tabbas na siyasa.