✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Doyin Okupe ya yi murabus daga kwamitin yakin neman zaben Peter Obi

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kama shi da laifin karkatar da kudaden makamai a zamanin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.

Tsohon Hadimin tsohon shugaban kasa kan Hulda da Jama’a, Doyin Okupe , ya sauka daga matsayinsa na Darakta-Janar na Yakin Neman Zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP.

Okupe ya yi murabus ne bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kama shi da laifin karkatar da kudaden makamai a zamanin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.

Ya sanar da saukarsa daga mukaminsa na Darakta-Janar na Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na LP ne ta wata wasika da ya aike wa dan takarar jam’iyyar, Peter Obi.

A ranar Litinin kotu ta yanke wa Okupe hukuncin dauri a gidan yari kan lafin karkatar da kudaden makamai a zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Mai shari’a Ijeoma Ojukwu, ta kama shi da laifuka 26, sannan ta yanke mishi hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari a kan kowanne laifi.

Ta kuma ci shi tarar Naira miliyan 13, tare da ba shi zabin biyan Naira dubu 500 a maimakon kowane hukuncin da ta yanke mishi na zama a gidan yari.

Sai dai ta ce idan ya gaza biyan tarar kafin karfe 4:30 na yammacin ranar Litinin, za a tisa keyarsa zuwa gidan yari.

A 2019, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta gurfanar da Doyin Okupe a gaban kotu kan tuhume-tuhume 59 kan halasta kudaden haram da karkatar da Naira miliyan 240 daga hannun Kanar Sambo Dasuki, tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Harkokin Tsaro.

EFCC ta gurfanar da tsohon hadimin shugaban kasan ne tare da wasu kamfanoni biyu: Value Trust Investment Ltd da Abrahams Telecoms Ltd.

Alkalin kotun ta ce ta yanke hukuncin ne bayan sauraron koken neman sassauci da wasu manyan ’yan Najeriya da suka hada da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Chukwuemeka Ezeife da kuma Shugaban Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA), Idi Farouk da matar Okupe, molara da kuma dansa.

A cewarta Okupe ya yi jayayyar karbar miliyoyin kudaden da ake zargin sa da karkatarwa.