DPO ya rasu a hatsarin mota bayan taron samar da tsaro a Katsina | Aminiya

DPO ya rasu a hatsarin mota bayan taron samar da tsaro a Katsina

    Abubakar Muhammad Usman da Tijjani Ibrahim, Katsina

Baturen ’Yan Sanda na yankin Musawa a Jihar Katsina, DSP Sabo Umar, ya mutu a wani hatsarin mota a ranar Laraba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya ce marigayin ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya ke dawowa Musawa daga Katsina, bayan halartar wani taro da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar da sauran hukumomin tsaro suka gudanar.

“Marigayi DPO yana nan tare da sauran jami’an gundumar tsaro na farin kaya DSS, da sauran jami’an tsaro don kammala shirye-shiryen aiki dangane da sabbin matakan tsaro da Gwamnatin Jihar Katsina ta dauka, tare da Kwamishinan ’Yan sanda, CP Sanusi Buba, a matsayin Shugaban Kwamitin Aiwatarwa.

“Bayan ganawar, DPO a kan hanyarsa ta komawa Musawa, kilomita 10 da Karamar Hukumar Matazu, ya yi taho mu gama da babbar mota kuma a nan ne ya rasa ransa,” inji Isah.

Kakakin ’yan sandan ya kara da cewa an ajiye gawar marigayin a Babban Asibitin Katsina kafin a kai shi garinsu da ke Karamar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato don yi masa sutura.

Isah, ya yi godiya ga Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, kan tallafi da ya ba wa iyalan mamacin da kuma motar daukar marasa lafiya da za a kai gawar zuwa Jihar Sakkwato.