✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ce abokiyar hamayarmu a Kano ba APC ba —NNPP

Jam'iyyar ta zargi cewar DSS na hada kai da APC don murde zabe a jihar.

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta bayyana cewa Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ce babbar abokiyar hamayarta ba APC ba.

NNPP ta yi zargin hukumar na aiki tare da jam’iyyar APC mai mulkin jihar domin tauye muradin jama’a a zaben gwamna da za a gudanar a ranar Asabar.

Da yake jawabi a madadin NNPP, Baffa Bichi, dan takarar kujerar Sanata a jam’iyyar, ya ce magoya bayan NNPP sun shirya tattaki na lumana a fadin jihar don nuna rashin amincewarsu kan ci gaban Daraktan DSS da zama ofishinsa bayan lokacin ritayarsa ya yi, wata 15 da suka shude.

Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bukaci a aike da daraktan  DSS din a 2017, sannan shi ya roki ya ci gaba da zama duk da karewar wa’adin aikinsa.

Ta kuma yi zargin cewa an aike da wasu jami’an DSS na musamman daga Abuja don taimaka APC wajen murde zabe.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne DSS ta sanar da kama wasu magoya bayan NNPP guda biyu kan zargin yunkurin tada tarzoma gabanin zaben ranar Asabar.

Kakakin DSS, Peter Afunanya, ya sanar a ranar Alhamis cewa an kama Sharu Abubakar Tabula da Isma’il Iliyasu Mangu ne kan zargin su da tunzura jama’a a kafafen sada zumunta.

Takun sakan DSS da NNPP

A baya dai an samu rashin jituwa tsakanin NNPP da DSS tun bayan da matar Darakta-Janar na DSS, Yusuf Bichi, ta yi sa-in-sa da dan takarar gwamnan Kano a NNPP, Abba Kabir Yusuf.

Rikicin ya fara ne bayan da ayarin motocin Abba sun tare wa ayarin matar Yusuf Bichi hanyar shiga dakin manyan baki a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Hakan ta kai ga cece-ku-ce tsakanin matar shugaban DSS din da wasu magoya bayan NNPP kafin daga bisani jami’an tsaro suka shiga tsakani.

Gabanin zaben shugaban kasa, DSS ta kai samame ofishin NNPP a Kano, abin da jam’iyyar ta zargi jami’an DSS da neman shafa wa magoyanta kashin kaji.