✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta cika hannu da ma’aikatan bankin da ke cuwa-cuwar sabbin kudade

DSS ta kama mutanen ne a Kano da Legas da Abuja da Fatakwal

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS da sanyin safiyar Litinin ta ce jami’anta sun kama wasu jami’an bankuna da ke cuwa-cuwar sabbin takardun kudi.

DSS ta ce ta kama jami’an ne a wasu manyan garuruwa da ke Jihohin kano da Legas da Ribas da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kakakin hukumar, Peter Afunanya ne ya tabbatar da kamun ranar Litinin a cikin wata sanarwa.

Ya ce daukar matakin ya zama wajibi ne la’akari da yadda mutane ke yi wa harkar rarraba takardun da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke yi zagon kasa.

A cewarsa, “Bincike ya nuna wasu jami’an bankunan kasuwanci suke taimakawa wajen kara tsananta wahalar kudi. Haka ne ya sa hukumarmu ta gargadi masu yin haka su bari ko kuma su kuka da kansu.

“Muna kuma kira ga jami’an tsaron da abin ya shafa da su dada sanya idanu domin tabbatar da an hukunta wadanda suka yi kunnen kashi,” in ji Afunanya.

Ya kuma ce hukumar ta umarci dukkan jami’anta da su tabbatar da ganowa tare da hukunta masu aika-aikar.

Daga nan sai Kakakin na DSS ya bukaci dukkan jama’a da suke da kowane irin bayani da zai taimaka wajen kama irin wadannan mutanen da su taimaka wa hukumar da su da ma sauran hukumomin tsaro.