✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta kama matasa 5 da suka yi garkuwa da mai shekara 6 a Kano

Dubunsu ta cika ne lokacin da suka kira domin karbar kudin fansa.

Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wasu matasa su shida da ake zargi da sace wani yaro mai shekara shida a duniya, Abdallah Abdulkadir Salisu na unguwar Gadon Kaya a Jihar Kano.

Kafar Prime Time News ta rawaito cewa wadanda ake zargin dai dukkansu mazauna unguwar Dorayi ne a Kano, kuma shekarunsu ba su wuce tsakanin 16 zuwa 21 ba.

A cewar kafar, dubun matasan ta cika ne lokacin da suka kira mahaifin yaron, Alhaji Abdulkadir Salisu domin karbar kudin fansa.

Jami’in hukumar ta DSS wanda ya jagoranci kama wadanda ake zargin amma ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin yafaru ne ranar 16 ga watan Yulin 2021, lokacin da wani mai suna Abdulhadi Ibrahim wanda dan uwan yaron da aka sace ne ya hada baki da abokansa da nufin sace shi don su sami kudin yin shagalin Babbar Sallah.

A cewarsa, lokacin da Abdulhadi ya sami nasarar sace yaron kasancewar yana shiga gidansu, sai ya kira wasu abokansa; Yusuf Abubakar da Adamu Shehu inda suka kai shi wurin da suka boye shi a kan babur mai kafa uku na Adaidaita Sahu.

Yaron dai ya ci gaba da zama a hannunsu har tsawon kwana uku, yayin da ake ci gaba da ciniki da mahaifinsa.

Ya ce da farko dai sun bukaci a basu Naira miliyan biyar, amma da ciniki ya kankama sai suka amince za su karbi N150,000.

Jami’in ya ce hukumar ta sami korafin sace yaron ne daga mahaifinsa, inda ya ce ba su yi wata-wata ba wajen fara bibiyarsu har zuwa lokacin da suka kama su yayin biyan kudin fansa.

Ya ce sun sami nasarar kubutar da yaron daga hannun masu garkuwar ba tare da ya ji ko da kwarzane ba, yayin da su kuma ake ci gaba da tsare su a ofishin hukumar da ke Kano.

Tuni dai iyayen masu garkuwar suka yi kudi-kudi suka tara N150,000 domin biyan mahaifin yaron a madadin kudin fansar da ’ya’yansu suka karba daga hannunsa.