✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

DSS ta kama Yahudawan Isra’ila 3 bisa zargin alaka da IPOB

Rahotanni sun ce Yahudawan sun zo Najeriya ne domin daukar wani fim.

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta cafke wasu Yahudawan Isra’ila uku bisa zarginsu da alaka da kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB.

An cafke mutanen ne wadanda suka hada da wani mai fafutukar kare Yahudawa, Rudy Rochman, da wani dan fim mai suna Noam Leibman, sai kuma wani dan jarida, David Benaym.

DSS dai ta kama su ne ranar tara ga watan Yuli lokacin da suka ziyarci Karamar Hukumar Idemili ta Arewa a Jihar Anambra.

Rahotanni sun ce Yahudawan sun taso ne daga filin jirgin sama na Ben Gurion da ke Isra’ila ranar biyar ga watan Yuli sannan suka iso Najeriya kashegari da nufin daukar wani fim da aka yi wa lakabi da ‘We Were Never Lost’.

Fim din dai na yunkurin zakulo yankunan da ke da alaka da Yahudawa ne a nahiyar Afirka kamar Kenya, Madagascar, Uganda, da kuma Najeriya.

Jaridar Times ta Isra’ila ta rawaito cewa ya zuwa yanzu, hukumomin Najeriya ba su kai ga tuhumar Yahudawan a kotu ba ko a basu damar daukar lauyoyi.

Jaridar ta ce an cafke masu shirya fim din ne bisa zargin sun zo ne da hadin bakin ’yan awaren na IPOB.

Kazalika, wata sanarwa ta ambato wasu daga cikin iyalan mutanen na zargin cewa ’yan siyasar Najeriya sun juya akalar kyautar littafin Attaura da suka bayar a yankin a matsayin yunkurin taimaka wa kokarinsu na ballewa.

Sun ce masu shirya fim din sun kawo kyauta ne ga yankunan da suka karbi bakuncinsu, amma sai aka canza wa kyautar ma’ana zuwa tallafa wa IPOB.

“Tawagar masu shirya fim din sun yi tunanin cewa zai kasance abu mai kyau idan suka ba mutanen kyaututtuka masu kayatarwa, kuma na tarihi,” inji sanarwar.

“Sai dai abin takaici, wasu ’yan gaza-gani sun yi amfani da siyasa wajen daukar hoton lokacin da ake ba da kyautar litattafan ga mutanen zuwa wani abin daban.”