✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

DSS ta sake gayyatar Mailafia

Karo na uku ke nan DSS ke gayyatar sa domin amsa tambayoyi

Hukumar tsaro ta DSS ta sake gayyatar tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Obadiah Mailafia a karo na uku domin amsa tambayoyi.

Mailafia wanda tsohon dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar ADC ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a.

“Gaskiya ne an gayyace ni zuwa ofishinsu na Jos. Sun ce min in je ranar Litinin da karfeh 11 na safe”, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito shi.

Tun bayan wata hira da aka yi da Mailafia a gidan radiyo wanda a ciki ya yi wasu zarge-zarge da ya karyata daga baya yake ta amsa tambayoyin DSS da ‘yan sanda a lokuta daban-daban.

Mailafia ya tayar da kurar a hirarsa da gidan radiyon Nigeria Info, inda ya yi zargin cewa wani gwamna mai ci a Arewacin Najeriya ne shugaban kungiyar Boko Haram.

Ya ce wani tubabben kwamandan kungiyar da suka tattauna da shi ya kuma shaida masa cewa sun hada baki da ‘yan bindiga kuma suna shirin tayar da zaune-tsaye a Najeriya.

Har ya ce ‘yan bindiga sun yi ta safarar makamai da kudada a cikin jirage zuwa sassan Najeriya a lokacin dokar kullen COVID-19 tamkar babu dokar.

Tun a lokacin masu sharhi ke ta kira da abinciki zargin nasa domin tabbatar da gaskiyar lamarin a yi wa tufkar hanci.

Bayan DSS ta yi masa tambayoyi, ya ce yana kan bakarsa kafin daga baya ya shaida wa BBC cewa dukkanin zarge-zargen da yi a hirarsa da Nigeria Info ba gaskiya ba ne, kuma a kasuwar kauye aka gaya masa.

Bayan DSS ta yi masa tambayoyi kan lamarin a karo na biyu ‘yan sanda suka gayyace da cewar za su yi masa nasu tambayoyin, lamarin da ya ce ba zai yiwu ba.

A watan Jiya ya shigar da kara gaban Babbar Kotu a Jihar Filato yana neman abin da ya kira hakkinsa na ‘yancin kai da in ta bangarensa domin hana ‘yan sanda yi bincikarsa.