✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta saki mawakin da ya yi wakar batanci a Kano

Matashin ya bayyana nadamarsa bayan da DSS ta turke shi na tsawon kwanaki.

Hukumar tsaron Farin Kaya (DSS) a Jihar Kano, ta sako mawakin nan da ta tsare, kan wakar batanci ga addinin Musulunci da ya fitar.

DSS ta ce ta turke mawakin a wani wurin tsare jama’a mai cike tsattsauran matakan tsaro domin gudun kada al’ummar gari su afka masa, musamman ganin yadda wakar batancin tasa ta yamutsa hazo a Jihar. 

Sai dai bayanai sun ce, mawakin ya nuna nadama tare da neman gafarar daukacin al’ummar Musulmi da Gwamnatin Jihar Kano da ma malaman Musulunci.

Ya shaida wa hukumar ta DSS cewa bai san wakar ta saba da koyarwar Musulunci ba.

Da yake tabbatar da lamarin a ranar Litinin, Sakataren Hukumar Tace Finai-finai ta Kano, Ismaila Afakallah, ya ce ya samu daruruwan sakonnin korafi daga jama’ar gari a kan wakar.

Malam Afakallah ya ce a kan haka ne ya mika rahoton mawakin ga hukumar ta DSS, inda jami’anta suka kama shi a wani otel din da yake boye tsawon lokaci.

Sai dai Afakalla ya ce a yanzu matashin ya koma hannun danginsa bayan kwashe tsawon kwanaki a tsare.

“An sake shi bayan ya yi nadama kuma ya nemi afuwa kan laifin da ya aikata tare da shan alwashin ba zai sake maimaita hakan ba a gaba,” a cewar Afakallah.

Dangane da dalilin da ya sanya Hukumar ba ta gurfanar da mawakin ba, Afakallah ya ce ba ita ce a gabansu ba, face ganin mutanen da suka aikata laifin sun tuba kuma sun yi nadama.

Wannan ba shi ne karo na farko ba da ake samun makamancin wannan lamari na samun mawaki da rera wakar batanci ga addinin Islama a Jihar Kano.

Ana iya tuna cewa a watan Agustan bara ce wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zama a unguwar Hausawa Filin Hockey a birnin Kano, ta samu wani matashin mawaki mai suna, Yahaya Sharif-Aminu, da laifin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) ta kuma yanke masa hukuncin kisa, kan yada wakar da ya yi a kafar WhatsApp.