✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta saki Yahudawan da ta kama bayan shafe kwana 20 a tsare

Tun da farko dai an zargesu ne da alaka da IPOB.

Hukumar Tsaro ta DSS ta saki Yahudawan Isra’ila uku masu shirya fina-finan da ta kama bayan shafe kwana 20 a tsare a hannunta.

Daya daga cikin manyan jami’an hukumar ne ya tabbatar da sakin nasu bayan an kammala bincike tare da tabbatar da cewa basu da alaka da zargin da ake musu na alaka da kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB.

An dai cafke mutanen ne wadanda suka hada da Rudy Rochman, da Noam Leibman da kuma David Benaym ranar tara ga watan Yulin 2021.

DSS dai ta kama su ne lokacin da suka ziyarci Karamar Hukumar Idemili ta Arewa a Jihar Anambra.

Rahotanni sun ce Yahudawan sun taso ne daga filin jirgin sama na Ben Gurion da ke Isra’ila ranar biyar ga watan Yuli sannan suka iso Najeriya kashegari da nufin daukar wani fim da aka yi wa lakabi da ‘We Were Never Lost’.

Fim din dai na yunkurin zakulo yankunan da ke da alaka da Yahudawa ne a nahiyar Afirka kamar Kenya, Madagascar, Uganda, da kuma Najeriya.