✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

DSS ta yi wa manyan mutane kashedi kan ta da fitina

DSS ta ce za ta kama duk babban mutumin da ke neman jefa kasa cikin rikici

Hukumar tsaro ta DSS ta sha alwashin kama duk wani babban mutum ko kungiyar da ke yada kalaman da ka iya jefa kasa cikin rikici.

Gargadin ca cikin takardar da kakakinta Peter Afunanya, ya fitar ya zargin tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Obadiah Mailafiya da neman tayar da zaune tsaye.

“DSS ba za ta tsaya tana kallon mutane suna daukar doka a hannunsu ba saboda rashin jin dadin wani abu ko bacin rai.

“Ba zamu yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani mutum ko kungiya da ke aikata laifi komai mukaminsa,” inji Afunanya

Mailafiya ya yi zargin cewa wani gwamna a Arewacin Najeriya ne shugaban kungiyar Boko Haram, a hirar da ya yi wata tashar radiyo.

Bayan ofishin DSS da ke Jihar Filato ya yi masa tambayoyi kan zargin da ya yi, Mailafiya ya ce yana nan kan bakarsa.

Sai dai daga baya ya janye maganar yana mai bayar da hakuri da cewa asuwar kauye ya tsinci maganar.

Obadiah Mailafiya, Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Takardar da DSS ta fitar a ranar Juma’a ta ce Mailafiya ya dade yana neman gafara kalaman da ya yi a ofishinta da ke Jihar Filato.

Ta misalta kalaman Mailafiya a matsayin biye wa mutanensa na tayar da fitina, da tabbacin mutanensa na niyyar daukar doka a hannunsu.

Ya ce, a matsayin mailafiya na tsohon Mataimakin Gwamnan CBN kuma ma’aikaci a Cibiyar Koyon Mulki ta Kasa (NIPSS) da ke Kuru, yana da hanyar gabatar da korafinsa ga gwamnati.

“A matsayinsa, ya kamata a ce ya san hanyoyin gabatar da korafinsa a gwamnatance, amma abun takaici sai ya zabi bin hanyar da bai kamata babban mutum kamarsa ya bi ba.

Ya koka cewa Mailafiya bai yi amfani da damarsa ba ya sanar da jami’an tsaro ko wata hukumar tsaro bayanan da ya ce ya ji ba.

“Ya yarda cewar abun da ya yi babban kuskure ne, saboda haka ana ganin ya yi kalaman nasa domin batanci da amfani da kalaman karya domin harzuka mutanen da ke jin maganarsa”, inji Afunanya.

Ya kuma yi Allah-wadai da maganar da Mailafiya ya yi na cewar yana nan kan bakarsa duk da tubar da ya yi a ofishinsu na jihar Filato.

“DSS na gargadin sauran mutane da ke taruwa a matsayin Kungiya ko taron siyasa, suna yin kaskanci ga gwamnati su daina haka nan,” inji shi.