✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun kawaliyar kananan yara ta cika a Delta

Tana yaudarar yara tana saka su karuwanci da sunan samar musu aiki.

Dubun wata mata ta cika bayan da aka kama ta bisa zargin yaudarar ’yan mata tana saka su karuwanci da sunan aiki a Jihar Delta.

Asirinta ya tonu ne bayan da ta yaudari wasu ’yan mata hudu, inda ta dauke su daga Jihar Akwa Ibon zuwa Delta da nufin samar musu aiki a mashaya.

Bayanan ’yan sandan yankin sun nuna matar takan yi amfani da yaran ne wajen karuwanci, inda ake biyan ta N1,000 zuwa N2,000 kafin a kwanta da su.

’Yan matan, wadanda shekarunsu ba su wuci 13 zu 15 ba, sun fada wa ’yan sanda cewa, Naira 400 kacal matar kan ba su a rana a matsayin kudin abinci, sannan ta rike wa kanta sauran.

Yaran sun ce sun bi matar ce a kan za ta nema musu aiki a masahaya don ba su damar samun abun biya wa kansu bukutu, musamman kuma kasancewarsu daliban jami’a.

Sun ce sun yi yinkurin tserewa sau da dama amma ba su yi nasara ba, kuma takan gana musu azaba kan haka aka ta kuma tilasta musu shan rantsuwa a gaban boka kan ba za su tsere ba.

An tsare matar ce a Jihar Anambra tare da gurfanar da ita a Kotun Majastre mai zamanta a Awka.

Kotun ta hana belin matar, kana ta ba da umarnin a ci gaba da tsare ta.