✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun mai damfara da sunan Ahmed Musa ta cika

’Yan sandan Kano sun kama mai damfarar matasa da sunan kyaftin din Super Eagles

’Yan sandan a Jihar Kano sun kama wani matashi da ke damfarar mutane a jihar da sunan Ahmed Musa, kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya.

Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama matashin ne bisa laifin damfarar mutane.

“Bayan an yi wa Kwamishinan ’Yan Sanda CP Habu A. Sani korafi, nan take ya ba da umarnin cafko wanda ake zargin a karkashin jagorancin CSP Abdulkarim Abdullahi.

“A ranar 20/12/2020, an yi nasarar cafke wanda ake zargin, inda ya amsa laifin nasa nan take.

“Ya bayyana cewa ya damfari mutum sama da 15 da ya sayar musu da takarda a kan kudi 5000.

“Ya damfari mutane kudi sama da 700,000 inda ya kashe wa ’yan matansa a otal a unguwar Sabon Gari,” inji Kiyawa.

Musa Muhammad daga unguwar Hotoro a Kano ne ya shigar da korafi a kan wanda ake zargin, wanda tsohon ma’aikacin wajen motsa jiki ne mallakar Ahmed Musa.

Wanda ake zargin ya amsa cewar yana damfarar matasa ne dake son tafiya kasashen ketare buga kwallon kafa da sunan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles.