✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun masu yi wa ’yan bindiga safarar man fetur a Sakkwato ta cika

Ana zargin gidan man ne da sayar da mai a jarkoki da tsakar dare ga 'yan bindiga.

Sashen da ke kula da hana lalata kayayyakin gwamnati na hukumar tsaro ta NSCDC a Jihar Sakkwato ya cafke wasu mutum biyu kan zargin yi wa ’yan bindiga safarar man fetur a Jihar.

Dubun mutanen dai ta cika ne ranar Juma’a da misalin karfe 2:00 na rana lokacin da jami’an hukumar suka kama su a gidan man Anasiyya da ke Karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa da ke Jihar.

Mataimakin Kwamanda mai kula da shiyyar Sakkwato na hukumar, Aminu Maijegi, wanda shi ne ya jagoranci kai farmakin ya shaida wa wakilin Aminiya cewa sun sami bayanan sirri ne tun da farko kan ayyukan gidan man daga jama’ar gari.

“Mun sami rahoton sirri da ke cewa gidan man na sayar da fetur a cikin jarkoki da tsakar dare, lamarin da ya saba da dokar da aka kafa a Jihar,” inji shi.

“Su kan kashe fitilun gidan ta yadda babu wanda zai yi zargin wani mummunan abu na faruwa a wajen.

“Bayan mun sami bayanan, sai na jagoranci jami’an hukumarmu zuwa wajen inda muka buya muna kallon abin da ke faruwa na kusan tsawon sa’a daya kafin mu dirar musu.

“A lokacin har sun riga sun cika sama da jarkoki 100 da man fetur. Duka mun kama su har ma da motar da take kokarin yin dakonsu ga ’yan bindigar zuwa Gabashin Jihar.

“Mun sami nasarar kama mutum biyu, Jabir Abubakar mai kimanin shekara 23 daga yankin Bazza, sai kuma Isiya Abubakar mai shekara 38 na Kofar Marke, dukkansu a Karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa, yayin da wani Malam Mustapha na kauyen Konnawa da ke Karamar Hukumar Dabge Shuni ya arce,” inji Mataimakin Kwamandan.

Ya kuma ce wadanda ake zargin sun amsa cewa suna shirin kai man ne zuwa Illela, wanda yana daya daga cikin yankunan da ’yan bindigar suka hana sakat.