✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun masu yunkurin garkuwa da mutane ta cika a Gombe

Dubun matasan ta cika ne lokacin da suke barazanar sace wani mutum

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta yi nasarar cafke wasu matasa uku da ake zargi da yunkurin yin garkuwa da mutane.

Wadanda ake zargin da yunkurin aikata laifin yin garkuwar su ne Danlami Abdullahi mai shekaru 30 da Maifata Galadima mai shekara 18 da kuma Fari Babangida mai shekara 22.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Ishola Babatunde Baba-Ita, a wani sako da ya aikewa manema labarai wanda ke dauke da sanya hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ne ya tabbatar da kamen.

Ya ce a ranar takwas ga watan Afirilu suka samu rahoto daga wani mai suna Malam Babayo Umaru na cewa a ranar 15 ga watan Maris, 2022, wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun boye lamba sun kira wani mutum suna masa barazanar za su yi garkuwa da shi.

Babatunde ya ce jami’an rundunar na sashen binciken sirri sun gudanar da binciken inda nan take suka gano mutanen kuma aka kamo su.

Kwamishinan ya ce binciken da aka yi  ya tabbatar da mutanen sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa.

Kwamishinan ’yan sandan ya Kara da cewa yanzu haka suna kan gudanar da bincike kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Daga nan sai Kwamishina Ishola ya yi kira ga al’ummar jihar Gombe da su dinga sanya ido akan duk wasu mutane da suke zargi, sannan su kiran jami’an yan sanda da zarar sun ga wani abin da ba su yarda da shi ba.