✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun matar da ke sayar da katin zabe ta cika a Enugu

An gurfanar da matar a gaban kotu, don girbar abin da ta aikata.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Enugu ta kama wata mata kan zargin ta da sayar da katin zabe a maimakon raba su ga ainahin masu su.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Daniel Ndukwe, ya fitar ranar Alhamis a Enugu.

“’Yan sanda daga sashen binciken manyan laifuka na Jihar Enugu a ranar 31 ga watan Janairu, 2023, sun kama wata mata da ake zargi, mai shekara 41.

“An ga matar a wani bidiyo da ya karade kafofin sada zumunta, inda ake zargin tana sayar da katin zabe na INEC a kan N1000 a wata makarantar firamare da ke Emene, a Jihar Enugu.

“Haka kuma an kama wata matashiya mai shekara 38, wadda aka bayyana cewa ma’aikaciyar INEC ce, wadda ake zargin ta da bayar da katin zaben ga wadda ake zargin da sayar da su domin rabawa masu katinan.

“An kammala bincike, an kuma mika lamarin gaban kotu bisa tanadin dokar zabe ta 2022, kuma wadanda ake zargin sun gurfana a gaban kuliya,” in ji shi.

Kakakin ’yan sandan ya kara da cewa, an bayar da belin wadanda ake zargin kuma an dage sauraren karar zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu, 2023.