✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun mutanen da suka hadiye kulli 165 na Hodar Iblis ta cika a Abuja

“Ba don kamun da aka yi min ba, da kimanin Dalar Amurka 1,000 zan samu in na kai kwayoyin Abuja.”

Mutum biyu sun yi kashin kulli 165 na Hodar Iblis din da suka hadidiye bayan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kama su a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.

Mutanen da aka kama din sun hada da Elvis Uche Iro mai kumanin shekara 53 da kuma Uwaezuoke Ikenna Christian mai shekara 42.

Elvis dai ya yi ikirarin cewa shi mai kawata gidaje ne, amma ya fada safarar miyagun kwayoyi don ya samu jarin fara sana’ar sayar da Coffee.

Ya ce ya yi hakan ne don ya samu ya kula da iyalansa, sannan ya samu kudin makare sabon shagonsa da ke Legas da kaya.

Ya ce ba don kamun da aka yi masa ba, da kimanin Dalar Amurka 1,000 zai samu in ya kai kwayoyin Abuja.

An dai kama shi ne da kulli 65, mai nauyin kilogiram 1.376 na Hodar, bayan saukarsa a filin daga birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Shi kuwa a nasa bangaren, Uwaezuoke an kama shi ne bayan ya hadiye kulli 100 na Hodar Iblis din, wacce nauyinta ya kai kilogiram 2.243.