✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun wani dan bindiga ta cika a Sakkwato

Jami'an tsaron sun dade suna nemansa kafin ya shiga hannu.

Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC), ta cafke wani da ake zargin dan bindiga ne a Jihar Sakkwato.

Mista Saleh Dada, Kwamandan NSCDC a Jihar ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewar wanda ake zargin mai shekara 40, yana daga cikin wadanda hukumar ke nema ruwa a jallo.

  1. Lambar NIN: Za a yi wa ’yan Najeriya da ke Amurka rajista
  2. Shari’ar El-Zakzaky da matsarsa: An tsaurara tsaro a Kaduna

Dada, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Talata a maboyarsa da ke garin Aliyu Jodi a cikin garin Sakkwato.

Kwamandan ya kara da cewa, an kama shi ne lokacin da ya fito siyan magunguna wadanda galibi na kara karfin maza ne ga mambobin kungiyar tasu.

Kazalika ya bayyana cewa, sun samu nasarar cafke mutumin biyo bayan samun bayanan sirri da jami’an tsaron suka dade suna dana masa tarko.

Kwamandan ya yaba wa al’umma kan yadda suka bayar da bayanan irin kalubalen tsaro a yankunansu tare da ba su tabbacin samun cikakken tsaro.