✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun wasu barayi a ATM ta cika

Dubun wasu masu damfarar mutane da suka kware wajen amfani da bayanan da suke nada ta Na’urar Cirar Kudi (ATM) da sabunta layin waya a…

Dubun wasu masu damfarar mutane da suka kware wajen amfani da bayanan da suke nada ta Na’urar Cirar Kudi (ATM) da sabunta layin waya a jihar Binuwai ta cika.

Jami’an Hukumar Yaki da cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun kwace katunan cirar kudi guda 31 a hannun mutanen, wadanda daya daga cikinsu ma’aikacin banki ne.

A cewar kakakin hukumar shiyyar Makurdi Dele Oyewale, jami’an hukumar sun cika hannu da mutanen ne a reshen bankin First Bank da ke Makurdi, kuma sun kware wajen zama a gefen na’urar ATM kamar za su taimaka wa masu zuwa cirar kudi.

Ya ce wadanda ake zargin wadanda dukkansu matasa ne sun hada da wani mai gadi a bankin.

Oyewale ya ce sauran kayan da aka kwace daga hannunsu sun hada da mota kirar Mazda, manyan wayoyi guda 10 sai kuma kananan wayoyi guda tara.

Sauran sun hada da layukan waya har guda 16, na’urar shiga yanar gizo ta kwamfuta (modem) da kuma kudade na jabu.

EFCC ta ce yanzu haka ta dukufa bincike kan wadanda ake zargin kuma za ta gurfanar da su gaban kuliya da zarar ta kammala.