✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubunsu ta cika bayan sun yanke kan wata mata

Sun yaudari wata mata sun yanke mata kai.

’Yan sanda sun cafke wasu mutum biyu dauke da kan dan Adam sabon yanka.

An kama mutanen ne bisa zargin yanke kan wata mata da suka kashe a unguwar Ayekale da ke yankin Saki a Jihar Oyo.

Wakilin Aminiya ya gano cewa wadanda ake zargin sun kashe matar ce bayan daya daga cikinsu ya yaudare ta ta hanyar kiran ta a waya.

Kakakin ’yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya ce an kai gawar matar dakin ajiyar gawa, ana kuma ci gaba da gudanar da bincike a kan abin da ya faru.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Oyo ta ce mutanen biyu na tsare ana bincikar su kan abin da ya faru.

Osifeto ya roki jama’ar jihar da su rika taimaka wa ’yan sanda da bayanai domin yakar masu aikata miyagun laifuka.