✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk da matsalar tsaro Buhari ya fi shugabannin baya – Sheik Jingir

JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya ce duk da kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fi shugabannin baya.

Shugaban Malisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Waikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya ce duk da kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fi shugabannin baya.

Ya bayyana hakan ne a karshen mako yayin bikin Musabaka na kungiyar karo na 24 da ya gudana a Gombe.

Shehin malamin y ace, “Mu na fuskantar kalubalen tsaro a kasa, amma duk da haka, halin da mu ke ciki a yanzu haka bai kai na baya tabarbarewa ba, lokacin da mutane ke dari-darin kusantar junan su.

“Ba wai ina nufin babu matsala ba ne ko komai na tafiya yadda ya kamata, amma alal hakika an sami ingantuwar harkokin tsaro,” inji shi

Sai dai malamin ya yi kira ga shugaban kan ya kara daura damara wajen yaki da aikata laifuka a kasa baki daya.

Kalaman malamin na zuwa ne kasa da mako daya bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari wata makarantar sakandire a garin Kankara na jihar Katsina tare da sace dalibai da dama, a daidai loacin da Buharin ke hutu a jihar.

Ko a kwanakin baya dai sai da ’yan ta’addan Boko Haram suka yi wa wasu manoman shinkafa 43 yankan rago a garin Zabarmari na jihar Borno.