✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk da tabbacin Buhari, Fasinjoijn jirgin kasa sun yi wata 6 a tsare

Ragowar mutum 23 da aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun shafe wata shida a hannun ’yan ta'adda, duk da alkawarin Shugaba…

Mutum 23 daga cikin fasinojijin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun shafe wata shida a hannun ’yan ta’adda da suka yi garkuwa da su, duk kuwa da da tabbacin da Shugaba Buhari ya bayar na ceto su.

Idan ba a lokacin da Buhari ya karbi bakuncin ’yan uwan fasinjojin da aka yi garkuwa da su ne ya ba su tabbacin yin duk mai yiwuwa domin ceto su ba tare da wani abu ya same su ba.

A ranar 28 ga watan Mari ne ’yan ta’adda suka kai harin bom a kan jirgin kasan da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, suka kashe kusan mutum 10 sannan suka yi gaba da wasu kimanin 60.

Bayan nan ne Buhari ya umarci manyan hafsoshin tsaro da su shiga farautar maharan sannan su kwato mutanen da aka sace ba tare da wani abu ya samu su ba.

An dai dora laifin harin jirgin kasan a kan gwamnati da kuma jami’an tsaro saboda rashin daukar matakan da suka dace kan bayan sirri.

Harin dai shi ne irinsa na biyu da aka kai wa jirgin kasan, bayan wanda ya auku a watan Oktoban 2021.

Ya kuma auku ne kwana kadan bayan wani hari da aka kai a Babban Filin Jirgin Sama da ke Kaduna, inda ’yan bindiga suka kashe wane jami’i.

Abin da gwamnati a ce

Bayan hari, manyan jami’an gwamnati irin su, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo; Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor; Babban Hafsan Sojin Kasa, Janar Faruk Yahaya; Shugaban ’Yan Sanda, Usman Alkali, suka ziyarci wurin da abin ya faru domin gane wa idonsu irin asarar da aka yi.

A lokacin da ziyarci wurin, Ministan Sufuri na lokacin, Rotimi Amaechi, ya shaida wa ’yan jarida cewa da an dauki shawarar da aka bayar a majalisar Zartarwa ta Kasa, da an magance aukuwar harin.

Ya bayyana cewa ya gabatar wa Majalisar shawarar sanya na’urorin samar da tsaro a kan lain jiring kasan, domin dakile yiwuwar kai hari, amma tatkwarorinsa suka yi fatali da bukatar.

A kamo ’yan ta’adda, a ceto mutane —Buhari

Bayan harin ne dai Shugaba Buhari ya la’anci maharan, tare da umartar jami’an staro da su kamo su, su ceto mutanen da ke hannunsu.

Kwanaki kadan bayan harin ne ’yan ta’addar suka sako Manajan Darkantan Bankin Manoma, Alwan Hassan, tare da wasu daga cikin fasinjojin.

Duk da cewa Hassan, wanda a wani bidiyonsa da ’yan bindigar suka saki yaci sun sake shi ne saboda tausaya masa, wasu majioyin sun ce sai da aka biya kudin fansa Naira miliyan N100 kafin a sako shi.

Mako biyu bayan harin dangin fasinjojin suk azargi Gwamnatin Tarayya da rashin damuwa da halin da suka shiga.

A nan ne suka bai wa gwamnatin wa’adin kwana uku at kubutar da su daga hannun ’yan ta’addar, idan ba haka ba, su za su zan hanyoyin da za su bi domin ganin an sako ’yan uwan nasu.

Har yanzu suna hannun ’yan ta’adda

yanzu wata shida ke nan da garkuwa da mutanen, kuma mutum 23 daga cikin mutanen da ’yan uwansu suka kasa biyan kudin fansa, na tsare a hannun masu garkuwa da su a cikin daji.

A baya dai, ’yan bindigar sun saki wasu daga cikin fasinjojin a cikin rukuni-rukuni bayan ’yan uwansu sun biya kudin fansa.

A kwanakin bayan Hukumar Tsaro ta DSS ta tsare Tukur Mamu, mutumin da ke shiga tsakani wajen karbo mutanen daga hannun ’yan bindiga.

DSS tsare dan jaridar ne bisa zargin sa ya karbi sama da Naira biliyan biyu daga iyalan fasinjojin kasan da aka yi garkuwa da su, ya kai wa ’yan ta’adda domin su sako mutanen da ke tsare a hannunsu.

Wata majiya ta ce akwai zarge-zarge masu yawa masu alaka da karbar kudaden fansar fasinjojin jirgin kasan, a kan Tukur Mamu.

“Ana zargin an samu bambanci tsakanin adadin kudaden da aka bia da abin daya kai wa masu garkuwar.

“Ana kuma zargin ya fi karkata zuwa bangaren ’yan ta’addan fiye da bangaren mutane da gwamnati.

“Abin da ya fi ban haushi a baya-bayan nan shi ne an yi maganar za a biya miliyan 25 domin sako mutane 23 da suka rage, amma sai da aka zo karshe, ya ce nemi a kara kudin,” in ji majiyar.