✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk da tsufata matashi ya yi mini fyade

Wata tsohuwa mai shekara 95 da aka yi wa fyade a Kwanar Dan Gora da ke Karamar Hukumar Kiru a Jihar Kano, ta ce ta…

Wata tsohuwa mai shekara 95 da aka yi wa fyade a Kwanar Dan Gora da ke Karamar Hukumar Kiru a Jihar Kano, ta ce ta shiga damuwa fiye da tunani.

A wata hira ta musamman da Aminiya,  tsohuwar wadda aka sakaya sunanta, ta kwatanta yadda abun da ya faru da abun da ya biyo baya da kuma yadda asirin matashin da ya yi mata ta’adin ya tonu.

— Ba zato ba tsammani

“Ranar Alhamis da daddare ina kwance a daki sai kawai aka shigo aka ce ‘dan ubanki kashe ki zan yi’, sai ni kuma na ce ai raina na hannun Allah.

“Ya ce wa zan gaya wa? Na ce da shi Allah. Ya ce ina kudi? Na ce babu kudi.

“Sai ya banke ni na fadi kwance, sai ya hau kaina ya buga mun wani abu a kirjina, ko mene ne ban sani ba, amma ina zaton wani abu ne ya buga mini.

“Sannan ne ya sa gwiyawunsa ya danne ni, ya makure wuyana, ya shake ni da karfin tsiya ko motsi ba na iyawa.

“Sannan ya yi abin da zai yi da ni, kuma bayan ya gama sai ya kwashe mini kudina kaf ya fita ya tafi.

—‘Irin lahanin da ni mini’

Tsohuwar ta kuma bayyana wa Aminya yadda ta shafe kwana 14 tana jinya bayan mutumin ya yi mata fyade ya tafi ya bar ta kwance sumammiya.

“A wannan lokacin na riga na suma ba san inda kaina yake ba, kuma ga shi gida ni kadai babu  kowa.

“Don haka da asuba ta yi sanyin asuba ya fara kadawa sai Allah Ya farfado da ni.

“Ko iya tashi ba na iya yi, don haka sai na yi rarrafe na je na buga wa makwabtana gida suka bude suka ga halin da nake ciki, kuma a sannan ko iya magana ba na yi.

“Matar mai anguwarmu da matan makwabtanmu su ne suka kai ni daki suka dafa ruwa sannan suka kai ni ban daki suka yi mini wanka tare da farsa jikina har na tsawon kwanaki goma sha hudu.


“Na zauna ko abinci bana iya ci sai dana wanda ke garin Makarfi [Jihar Kaduna] ya zo ya zauna tare da ni.

“Su kuma makwabta da matar mai anguwarmu su ne suke kula da ni suna mun farsan jikina da ruwan zafi har na tsawon lokacin da Allah Ya sa na sami lafiya, domin a lokacin ba na iya cin komai sai dai ruwan shayi ba madara, shi ma ba yai wuce dan cokali kadan.

— Duk da tsufata na shiga damuwa

“Tun daga lokacin, duk da tsufata amma na shiga damuwa kwarai a kan irin halin da na tsinci kaina da kuma yadda al’umma suke dauka ta da irin yadda aka yi masu bincike suke yawan ziyara ta domin neman bayanai.

—Mai fyade ya buwayi matan gari

“Ana cikin haka kwatsam sai Allah Ya sa aka ce an kama shi ya fito daga wurin muguwar sana’arsa da yake aikata wa  matan gari.

“Domin kafin a kama shi matan gari ba su da sukunin natsuwa domin babu wanda ya san shi sai dai kwatance kawai, don wasu matan ma na zaton aljani ne.

“Sai dai an rada masa suna wai Mai Siket, duk gari haka za ka ji ana cewa Mai Siket ya shiga gidan wane amma babu wanda ya san shi.

— Da kansa ya fadi abun da ya aikata

“Da Allah Ya tona masa asiri aka kama shi tsirara haihuwar uwarsa, shi da kansa ya ce shi ne ya shiga gidana ya aikata mun fyade kuma ya kwashe mun kudina.

To bayan nan an kai ni ofishin ’yan sanda a garin Kano, aka yi mum tambayoyi.

“Ni dai abin da nake bukata shi ne tun da har ya amsa da bakin sa cewa shi ne ya aikata mun fyade to ina bukata da a bi mini hakkina.

— Mun samu sa’ida, inji Mai unguwa

Da yake nuna farin cikin bakasa da asirin mai Siket ya tonu Mai Unguwa Alhaji Ahmadu Ya’u ya ce, “Da muna cikin damuwa amman yanzu muna cikin farin ciki da Allah Ya tona mana asirin wannan mugun yaron da ya firgita mana matan gari ciki har da makwabciyata  tsohuwa mai shekaru da yawa.

“Ya far mata ya bata ta domin kuwa har sai da ta kwashe tsawon lokaci tana jinya.