✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk da tubar dubban ’yan ta’adda a dage da addu’o’i —Zulum

Zuluma ya ce yawan addu'o'i ita ce hanyar da za ta samar da dauwamammen zaman lafiya

Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya nemi mabiya addinin Kirista da su yi amfani da bikin Ista wajen yin addu’o’i domin ci gaba da samun nasara da ake yi a kan ’yan ta’adda.

Gwamnan ya yi kiran ne a cikin sakonsa na taya Kiristoci murnar bikin Ista, ta wata sanarwa da kakakinsa, Isa Gusau, ya fitar a ranar Litinin.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Gwamnatin Jihar Borno ke gudanar da wani shirin gyara hali da ake wa dubban ’yan ta’addan Boko Haram da suka mika wuya.

Ya ce wannan hanya ce za ta iya samar da dawwamammen zaman lafiya a jihar.

“Babban muhimmancin Ista shi ne sadaukarwa da yafiya ga wadanda suka aikata laifuka da kuma zama tsintsiya madaurinki daya domin iya jure duk wani abu da ke iya zuwa.

“A cikin shekaru 12 da aka kwashe ana yaki da kungiyar Boko Haram da ISWAP, wannan shi ne karon farko da za a iya cewa matsalar tsaro tana gab da zuwa karshe a Jihar Borno.

“Samun ’yan ta’adda 35,000 tare da wasu kwamandodin su wani iko ne na Allah na dawo da zaman lafiya a Jihar Borno da ma Arewa maso Gabas ga baki daya.

“Wannan ya nuna irin kokari da jajircewa dama sadaukarwa da sojoji da masu taimakon su ke yi.

“Da ma irin kiraye-kiraye da manyan yan siyasa da malamai da sarakunan gargajiya ke yi ga yan ta’addan na ajiye makamansu domin samun zaman lafiya,”

Idan za a lura a wata uku da suka gabata an samu raguwar kai hare-hare a kan fararen hula, musamman garkuwa da mutane a kan hanyar Borno zuwa Damaturu da ’yan ta’addan suke.

Kwamandan rundunar soji ta “Operatin Hadin Kai” na Arewa maso Gabas, Manjo Janar Christopher Musa ya ce fiye ’yan ta’adda 50,000 tare da iyalansu ne suka mika wuya.