✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk da umarnin ’yan sanda, dubban magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kano

Tun daga Kwanar Dangora suka je tarbar Kwankwaso

Dubban magoya bayan NNPP sun tarbi dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso a Jihar Kano daga Kaduna.

Hakan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan fitar sanarwar Rundunar ’Yan Sandan Jihar kan dakatar da dukkan wasu gangamin siyasa a jihar, dalilin rikicin da ya balle tsakanin magoya bayan jam’iyyar ta NNPP da na APC.

Cikin wata sanarwa da Kakakin kwamitin yakin neman zaben dan takarar Gwamnan Jihar a jam’iyyar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce sai da NNPP din ta aika wa Kwamishinan ’Yan Sanda wasika cewa ba yakin neman zabe za su gudanar ba, tarbar dan takarar Shugaban Kasarsu da ya dawo Kano don gudanar da zabe suka yi.

Sunusi ya ce za su ci gaba da yin biyayya ga dokokin Najeriya, domin burinsu bai wuce a gudanar da sahihin zabe cikin lumana ba.

“Mun watsa shirin APC na hana magoya baya da masu ruwa da tsakin jam’iyyarmu morar ’yancin gudanar da harkokin siyasa da doka ta ba su dama.

“Mun kuma yi maraba da kokarin sojoji, da ’yan sanda, da Sibil difens na suka kama ’yan daba 300 da suka tayar da tarzomar.

“Mun samu labarin har shugabannin jam’iyyu na Kananan Hukumomi biyu aka kama da haramtattun bindigu.

“Haka kuma mun samu wani labarin cewa wani fitaccen dan daba da jam’iyya mai mulki a Jihar ke amfani da shi don tada hankali shi ma ya shiga hannun ’yan sanda.

“Da haka muke kira ga ’yan sanda da su tabbatar da cewa an gurfanar da duk wanda aka kamo a gaban kotu domin fuskantar fushin hukuma.