Duk daliget din da ya sayar da kuri’arsa ya hallaka – Sheikh Jingir | Aminiya

Duk daliget din da ya sayar da kuri’arsa ya hallaka – Sheikh Jingir

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir a Masallacin Idi na Tashar mota ta Bauchi road da ke garin Jos
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir a Masallacin Idi na Tashar mota ta Bauchi road da ke garin Jos
    Hussaini Isah, Jos

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce duk daliget din da aka ba shi kudi ya sayar da kuri’arsa, a wajen zaben fid-da- gwani na ’yan takara, ya hallaka.

Sheikh Sani Yahya Jingir, ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wa’azi a Masallacin Juma’a na ’Yan Taya, da ke Jos.

Ya ce abubuwan da ’yan siyasa masu takara da daleget suka yi, na amfani da kudi a wuraren zabubbukan fid-da-gwani na ’yan takara da jam’iyyu suka gudanar, abin kunya ne kuma abin tsoro ne.

Sheikh Jingir ya ce daleget din da aka ba su kudi, suka sayar da kuri’arsu sun kafa wa kan su, mugun tarihi domin sun sayar da ’yancin jama’arsu. Ya ce da daleget da ’yan siyasar da suka ba su kudi duk masu laifi ne.

“Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya sayar da kansa, ya hallaka. Daleget an tura ku ne don ku zabo mana shugabannin nagari, amma kun je an ba ku kudi kun sayar da ’yancin jama’a, saboda haka babu abin da za ku zo ku fada wa mutanenku, domin kun ci amanarsu,” inji shi.