✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk jam’iyyar da ta karya Dokar Zabe za mu hana ta zabe a 2023 —INEC

INEC ta ce duk jam'iyyar da ta yi sake za a yi babu ita.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta yi gargadin cewa duk jam’iyyar da aka samu ta sabawa kowane tanadi da Dokar Zabe ta yi, to kuwa ta kwana da shirin babu ita za a dama a zaben 2023 da ke tafe.

Kwamishinan INEC na Kasa kuma Shugaban Kwamitin Sadarwa da Wayar da Kai kan Harkokin Zabe, Festus Okoye ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

A cewarsa, duk jam’iyyar da aka samu ta yi wa wani sashe na Dokar Zabe karan-tsaye, to babu shakka za a cire sunan duk dan takarar da ta tsayar daga jerin wadanda za a kadawa kuri’a a babban zaben na badi.

Ana iya tuna cewa, a watan Fabrairun da ya gabata ne Hukumar INEC ta fitar da jadawalin babban zaben.

Hukumar ta ce za a gudanar da Shugaban Kasa da na yan Majalisar Tarayyar a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023.

Haka kuma, zaben gwamnoni da na ’yan Majalisar Dokoki zai gudana a ranar 11 ga watan Maris na 2023.

Wannan dai ya biyo bayan rattaba hannu kan sabon daftarin Dokar Zaben kasar da shugaba Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu, bayan shafe tsawon lokaci na cece-kuce kanta.