✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Duk mai son mukami a gwamnatina sai ya kawo akwatinsa yayin zabe —Atiku

Ya ce ba yawon kamfe ne kawai zai sa mutum ya sami mukami ba

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce duk dan jam’iyyar da ke neman kwagila ko mukami a gwamnatinsa, sai ya nuna sakamakon zaben mazabarsa kafin a ba shi.

Atiku ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abekuta babban birnin Jihar Ogun, yayin taron ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Atiku ya ce halartar kowanne yakin neman zaben jam’iyyar ba shi ne tabbacin samun matsayi ko kwangila a gwamnatinsa ba, jajircewa wajen ganin an kawo akwatinan mazaba ne.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya kuma ce, “Dukkanku magoya bayan PDP ne, kuma kuna so ta dawo mulki, don haka ina rokonku ku tabbatar kun kawo akwatinan mazabunku.

“Yawon zuwa yakin neman zaben kafatanin ’yan takarar jam’iyya ba shi ne zai sa ka samu aiki ko matsayi ko kwangila ba idan an ci zabe, hanyar da kadai za ku samu shi ne nuna min sakamakon zaben mazabarku.

“Kuma ina bai wa kowanne dan takarar PDP umarnin yin hakan, domin da haka ne kadai za mu ci zabe.

Atiku ya kuma yi alkawarin farfado da bangaren ilimi da tattalin arziki, domin kawo karshen yajin aikin jami’o’i a Najeriya, da kuma inganta rayuwar ma’aikata da sauran al’umma.