✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Duk Shugaban Kasar da zai zo zai fuskanci kalubale irin na Jonathan da Buhari’

Ya ce babu wasu alamu da ke nuna Shugaba mai zuwa zai sami bambanci

Wani masanin Kimiyyar Siyasa, Farfesa Jibrin Ibrahim, ya ce alamu na nuna Shugaban Kasar Najeriya na gaba zai fuskanci kalubale yadda Goodluck Jonathan da Muhammadu Buharibaya suka fuskanta.

Farfesan wanda malami ne a Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa na Jami’a’a r Abuja kuma jagora a cibiyar Dimokuradiyya da cigaba (CDD), ya yi gargadin ne yayin taron tattaunawa na kamfanin Media Trust, karo na 20 a Abuja.

A cewarsa, duk da cewa ’yan takarar sun yi  bayanai dalla-dalla kan abubuwan da suke son yi idan aka zabe su, sun gaza bayyana hanyoyin da za su bi wajen aiwatar da su.

Ya ce, “An tabo batun matsalar tsaro, da yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati da kuma raba tattalin arzikin kasa yadda ya dace, sai dai babu daya daga cikin ’yan takarar da ke da mahangar da ta bambamta da ta saura?

“Ina da masaniyar wadannen tsare-tsare rubuta su aka yi kamar yadda Jonathan ya zo ya yi nasa irin su, amma ya gaza cikawa, haka shi ma Buharin sai ma ya zama mun koma gara bara da bana.

“Aikin gwamnati a kasar nan ya lalace, cin hanci ya shiga ko ina, amma dukkaninsu ba wanda ya fadi yadda zai kawo karshensu a maufofinsa.

“Muna sane da cewa  manyan jam’iyyun kasar nan neman kudi ne kawai a gabansu, don haka sanin kowa ne idan ka shiga siyasa don satar kudin al’umma, maganar yakar cin hanci ma ba ta taso ba,” in ji shi.