✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Duk wanda aka yi wa lambar NIN kafin 2012 sai ya sake’

Lambobin NIN da aka bayar a farkon shekarun 2000 ba su da halarci

Hukumar Ba da Shaidar Zama dan Kasa (NIMC) ta ce duk  wanda aka yi wa rajistar katin shaida ko lambar dan kasa ta NIN kafin shekarar 2012 sai ya sake.

Babban Jami’in NIMC a Jihar Kwara, ya ce duk katunan shaidar dan kasa da ko lambar NIN da aka bayar kafin shekarar 2012 a Jihar ba su da amfani.

Ya bayyana cewa lambobin NIN da aka bayar a farkon shekarun 2000 ba su da halarci domin dokar da ta kafa Hukumar NIMC ba ta yarda da su ba.

Don haka ya yi kira ga duk wadanda ba su yi rajistar samun shaidar dan kasa ta NIN ba da su hanzarta yin hakan.

Popoola ya bayyana haka ne a lokacin da ya yake jawabi ga ‘yan jarida ranar Talata a Jami’ar Ilorin, Jihar Kwara.

Ya ce cibiyoyin rajistar NIMC a fadin Jihar za su kasance a bude a duk ranakun aiki domin yi wa jama’a rajistar shaidar zama dan kasa.

Ya kuma yaba da hadin kan da Hukumar ta samu daga jami’ar wadda ya ce ta ba wa NIMC cibiyar yi wa jama’a rajistar tun a shekarar 2004.